NLC Ta ba Gwamna Radda Wa'adi kan Shiga Yajin Aiki a Katsina

NLC Ta ba Gwamna Radda Wa'adi kan Shiga Yajin Aiki a Katsina

  • Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) reshen jihar Katsina ta gaji da jinkirin da ake samu kan biyan sabon mafi ƙarancin albashi
  • NLC ta yi barazanar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani idan har ba ta samu wata gamsashshiyar amsa daga wajen gwamnatin jihar ba
  • Shugaban NLC na Katsina, Kwamared Hussain Hamisu ya bayyana cewa za su shiga yajin aikin ne domin bin umarnin shugabannin su na ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) reshen Katsina ta yi barazanar ba gwamnatin jihar wa’adin zuwa ranar Talata kan shiga yajin aiki.

Ƙungiyar NLC ta ce idan har ba ta samu amsa mai kyau ba, za ta bi umarnin da shugabanninta na ƙasa suka bayar a taron da suka yi a birnin Port Harcourt.

Kara karanta wannan

Jigawa: Ma'aikata za su tsunduma yajin aiki kan rashin biyan sabon albashin N70000

NLC ta gargadi gwamnatin Katsina
NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki a Katsina Hoto: Nigeria Labour Congress HQ, Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Shugaban NLC na Katsina, Kwamared Hussain Hamisu, ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me NLC ta ce kan yajin aiki a Katsina?

Kwamared Hussain Hamisu ya bayyana damuwarsa kan jinkirin da ake samu a tattaunawa da gwamnatin jihar dangane da biyan sabon mafi ƙarancin albashin.

Ya kuma lura cewa ƙarin albashi ga ma'aikatan suka yi ritaya har yanzu bai tabbata ba, duk da kammala aikin da kwamitin da aka ɗorawa alhakin hakan ya yi.

"Aikin kwamitin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi da gwamnatin jihar ta ƙaddamar ya ƙare bayan cikar wa’adin da aka ɗibar musu."
"Idan har zuwa gobe Litinin babu wata amsa mai kyau daga gwamnatin jiha, za mu ayyana shiga yajin aikin sai baba-ta-gani, domin bin umarnin majalisar zartarwa ta NLC a taron da aka yi a Port Harcourt."

- Kwamared Hussain Hamisu

Za mu bi umarnin NLC

Shugaban NULGE na ƙaramar hukumar Danja, Alhaji Nura Rabiu, ya shaidawa Legit Hausa cewa za su bi umarnin NLC kan shiga yajin aikin.

Kara karanta wannan

Gwamna ya roki 'yan kwadago su hakura da shiga yajin aiki

"Idan har lamarin ya kai shiga yajin aiki, kuma mun samu umarni daga shugabannin mu, to za mu shiga."

- Alhaji Nura Rabiu

Gwamna ya roƙi ƴan ƙwadago

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Cross Rivers, Bassey Edet Otu, ya yi kira ga ƙungiyoyin ƙwadago na jihar da su haƙura da shiga yajin aiki.

Gwamna Bassey Otu ya buƙaci ƙungiyoyin ƙwadagon da su sake duba yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da za su fara daga ranar Lahadi, 24 ga Nuwamba zuwa Talata 26 ga watan Nuwamban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng