Tinubu Ya Karbo Bashin Naira Tiriliyan 5.63 daga Hannun ‘Ƴan Kasuwa, Ya Yi Ayyuka 2
- Gwamnatin Najeriya ta ciyo bashin Naira tiriliyan 5.63 daga masu saka hannun jari na gida ta hanyar 'FGN Bond' a watanni 11 na 2024
- Gwamnatin ta karbo bashin ne domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2024 da kuma aiwatar da wasu muhimman ayyukan kasa
- Hukumar gudanar da basussuka (DMO) ta yi karin haske kan yadda aka samu kudaden da kuma yadda aka rarraba su a kasuwar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin tarayya ta ciyo bashin Naira tiriliyan 5.63 daga masu saka hannun jari na gida ta cikin kasuwar 'FGN Bond' a shekarar 2024.
Wannan ya zarce Naira tiriliyan 5.6 da hukumar gudanar da basussuka (DMO) ta shirya karbowa, wanda ke nuna karuwar jarin 'yan kasuwar gidan.
Gwamnatin tarayya ta karbo bashin N5.63
Jimillar kudin da aka nema daga masu saka hannun jari ya kai Naira tiriliyan 6.81, saboda bukatar karin riba ta dogon lokaci, a cewar rahoton Arise News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce gwamnatin tarayyar ta karbo wannna bashin ne domin cike gibin kasafin 2024 tare da aiwatar da wasu muhimman ayyukan more rayuwa.
A watan Fabrairun 2024 ne ya aka fi samun tayin zuba jarin, kudaden da aka nema, da kuma rarraba jarin, yayin da aka samu raguwar hakan a Nuwamba.
Kudaden da gwamnati ta samu daga 'yan kasuwa
A watan Fabrairu, DMO ta nemi Naira tiriliyan 2.5 daga 'yan kasuwa, inda ta samu kudin jari na Naira tiriliyan 1.9 yayin da ta rarraba Naira tiriliyan 1.49.
A Nuwambar 2024, gwamnatin ta bukaci jarin Naira biliyan 120 daga 'yan kasuwar, an kuma raba shi dai-dai tsakanin jerin hannayen jari biyu.
Duk da karancin tayin da aka samu, adadin jarin da aka rarraba ya karu da kashi 19.5%, inda ya kai Naira biliyan 346.16 a Nuwambar shekarar.
Bankin Duniya ya ba Najeriya sabon bashi
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta samu rancen $500m daga Bankin Duniya domin karfafa kamfanonin Discos.
Kamfanin Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da samun kudin inda ya ce za ayi amfani da su domin aiwatar da shirin gyaran bangaren rarraba wutar lantarki (DISREP).
Asali: Legit.ng