Gwamnatin Tarayya za ta ba ‘Yan kasuwa bashi mai rahusa a Najeriya

Gwamnatin Tarayya za ta ba ‘Yan kasuwa bashi mai rahusa a Najeriya

Mun samu labari daga fadar Shugaban kasa cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta ba kananan ‘Yan kasuwa a Najeriya bashi ba tare da karbar jingina ba domin bunkasa harkar kasuwanci.

Gwamnatin Tarayya za ta ba ‘Yan kasuwa bashi mai rahusa a Najeriya
Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo yace 'Yan kasuwa za su amfana da Gwamnatin nan

Mataimakin Shugaban kasa ya bayyana cewa ‘Yan kasuwa mutum miliyan 2 za su amfana da wani tsari mai suna Trader Moni a karkashin shirin nan na GEEP na wannan Gwamnati wanda aka shirya domin karawa kananan ‘yan kasuwan kasar karfi.

Laolu Akande wanda ke magana a madadin Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yace kafin nan da karshen shekara za a ba ‘yan kasuwa miliyan 2 bashi domin su kara karfi a wajen sana’ar su. Har an kaddamar da wannan tsari a Legas.

KU KARANTA: An kashe sama da mutum 10 a cikin Jihar Adamawa

Za a zabi kananan ‘yan kasuwa 30000 ne a kowace Jiha da kuma Birnin Tarayya Abuja. Irin su Legas da Kano za su samu karin fifiko wajen wannan tsari saboda yawan al’ummar su. Bankin da ke kula da sha’anin masana’antu BOI ne zai yi wannan aiki.

A wannam tsari na Trade Moni, ‘Dan kasuwa zai iya samn bashin har N15000 zuwa N50000 idan har mutum ya biya kudin da aka fara ba sa. Gwamnatin Buhari ta kawo wannan tsari ne domin taimakawa kananun ‘Yan kasuwa da ke cikin Karkarori.

Dazu kun ji cewa Shugaban kasa Buhari ya taya tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Cif John Odigie Oyegun murnar zagayowar ranar haihuwar sa. John Oyegun ya cika shekara 79 a Duniya jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel