Kyaftin Ahmed Musa Ya Aika Sako ga Masoyansa da Ya Zama Jakadan Bankin Jaiz

Kyaftin Ahmed Musa Ya Aika Sako ga Masoyansa da Ya Zama Jakadan Bankin Jaiz

  • Fitaccen dan kwallon kafar Najeriya, Ahmed Musa, ya sanar da hadin gwiwarsa da bankin Jaiz a matsayin sabon jakadansa
  • Kyaftin Ahmed Musa ya bayyana jin dadinsa tare da godiya ga bankin bisa wannan babbar dama da ya ba shi na yin aiki tare
  • Dan wasan ya ce bankin Jaiz yana wakiltar ci gaba, tsaro, da karfafa ikon kudi na mutane yayin da ya aika sako ga masoyansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Fitaccen dan wasan kwallon kafar Najeriya, Ahmed Musa ya kara cimma wata gagarumar nasara a cikin aikinsa, wannan karon a bayan fage.

Kyaftin din kungiyar Super Eagles ya sanar da cewa ya kulla yarjejeniya da bankin Jaiz inda ya zamo jakadan bankin a yanzu.

Ahmed Musa ya yi magana yayin da ya zama jakadan bankin Jaiz.
Ahmed Musa ya aika sako ga masoyansa yayin da ya zama jakadan bankin Jaiz. Hoto: @Ahmedmusa718
Asali: Twitter

Ahmed Musa ya zama jakadan Jaiz

Da yake sanar da wannan ci gaba a shafinsa na X, Ahmed Musa ya nuna tsantsar farin ciki da kuma yiwa Allah godiya yana mai cewa:

Kara karanta wannan

Ta ya za a biya?: Dan siyasa ya fadi kuskuren Tinubu na karbo sabon bashin N1.7trn

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Alhamdulillah! Ina cike da farin cikin sanar da ku cewa zan yi aiki da bankin Jaiz a matsayin sabon jakadansu."

Kyaftin Ahmed Musa ya jinjinawa bankin Jaiz bisa jajircewarsa na samun ci gaba, tsaro da kuma karfafa hada hadar kudi.

"Abin alfahari ne na wakilci wannan babban banki wanda ya dora tsarinsa a kan wadannan muhimman abubuwa."

- A cewar Ahmed Musa.

Ahmed Musa ya aika sako ga masoyansa

Fitaccen dan wasan kwallon kafar ya aika sako ga magoya bayansa inda ya nemi su bude asusu da bankin Jaiz, wanda banki ne marar ruwa.

"Ku zo mu samu ci gaba tare," Ahmed Musa ya bukaci masoyansa yayin da ya ke nuni da wasu manyan ayyukan da zai yi tare da bankin nan gaba.

Bankin Jaiz, wanda ya yi suna a bangaren inganta jama'a ta hanyar samar da kudade, a yanzu ya hada gwiwa da daya daga cikin ’yan wasan da ake so a Najeriya, Ahmed Musa.

Kara karanta wannan

Nasarawa: Fada ya barke tsakanin makiyaya da manoma, an kashe mutane da dama

Ahmed Musa ya samu sarauta a Nguru

A wani labarin, mun ruwaito cewa keftin din tawagar kwallon Super Eagles, Ahmed Musa ya samu sarautar gargajiya ta 'Shetiman Kwallon Kafar Nguru'.

Sarkin Nguru, Alhaji Mustapha Ibn Mai Kyari ne ya naɗa fitaccen ɗan kwallon kafar wannan saurata bayan wata ziyara da ya kai fadarsa da ke Nguru, jihar Yobe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.