Yan Sandan Jiha: Shugaba Tinubu Ya ba Jihohin Arewa 3 Wa'adin Mako 1
- Akalla jihohi 33 ne suka mika rahoto kan matsayarsu game da kirkirar yan sandan jiha a Najeriya yayin da ake ta shirye shirye
- Kwamitin tattalin arziki (NEC) ya ba jihohi uku da suka rage da birnin Tarayya Abuja wa'adin mako daya kacal da su mika rahotonsu
- Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa shi ya ba da wannan wa'adi inda ya ce abin takaici ne har yanzu ba su mika rahotonsu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kwamitin tattalin arziki (NEC) ya ba birnin Tarayya Abuja da wasu jihohi uku wa'adi kan yan sanda jihohi.
Kwamitin ya ba da wa'adin mako daya ga jihohin Adamawa da Kwara da Kebbi domin sanin matsayarsu.
Jihohin da ba su mika rahotonsu ba
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da gargadin da Gwamna Douye ya Bayelsa ya fitar, cewar rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Diri ya ce jihohi uku ne kacal da birnin Tarayya Abuja har yanzu ba su mika rahotonsu kan kirkirar yan sandan ba.
Daga cikin jihohin da suka rage a Najeriya ban da birnin Abuja akwai Kwara da Adamawa da Kebbi, Punch ta ruwaito.
Yawan jihohin da suka ba da rahotonsu
Gwamnan ya ce a yanzu haka jihohi 33 a Najeriya sun gabatar da rahoton na su kan matsayarsu game da yan sandan jihohi.
"Kwamitin ya sabunta rahoton dukan jihohi inda aka samu akalla guda 33 sun mika rahotonsu yayin da guda uku ba su kawo ba."
"Jihohin guda uku sun hada da Kebbi da Adamawa da kuma abin mamaki Kwara inda gwamnan jihar ya ke riƙe da mukamin shugaban gwamnoni."
- Douye Diri
Yan sandan jiha: Tinubu ya ba jihohi 4 wa'adi
A labari mai kama da wannan, ana shirye-shiryen kirkirar yan sandan jihohi, an ba jihohi hudu wa'adin kwanaki biyar domin kawo rahotonsu kan lamarin.
Jihohin da ake zance sun hada da Adamawa da Kebbi da Sokoto da kuma jihar Kwara sannan da birnin Tarayyar Najeriya watau Abuja.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin gwamnan Oyo, Bayo Lawal ya fitar a ranar Laraba 4 ga watan Satumbar 2024.
Asali: Legit.ng