Dakarun Sojoji Sun Sheke Kwamandan 'Yan Ta'adda da Wasu 114

Dakarun Sojoji Sun Sheke Kwamandan 'Yan Ta'adda da Wasu 114

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda 115 tare da cafke wasu 238 a cikin mako ɗaya
  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta sanar da cewa daga cikin ƴan ta'addan akwai kwamandansu mai suna Munzur Ya Audu
  • Sojojin sun kuma kuɓutar da mutane 138 da ƴan ta'addan suka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojoji sun hallaka wani kwamandan ƴan ta'adda Munzur Ya Audu.

DHQ ta kuma sanar da cewa dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'adda 114 tare da cafke guda 238 a cikin mako ɗaya.

Sojoji sun hallaka kwamandan 'yan ta'adda
Dakarun sojoji sun hallaka kwamandan 'yan ta'adda Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Sojoji sun samu nasara kan ƴan ta'adda

Daraktan yada labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Sojoji Najeriya sun kama wani Alhaji da ke taimakawa ƴan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Edward Buba ya bayyana cewa an rasa jami'an sojoji takwas, biyar a yankin Arewa maso Gabas da uku a Kudu maso Gabas, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ya ƙara da cewan dakarun sojojin kuɓutar da mutane 138 da aka yi garkuwa da su a cikin mako guda.

A yakin da ake yi da satar ɗanyen mai, sojojin sun kama mutane 51 da ake zargin barayin mai ne tare da kwato man da kuɗinsa ya kai N921,847,146.00.

Sojoji sun kashe kwamandan ƴan ta'adda

Edward Buba ya bayyana cewa ce an kashe wani kwamandan ƴan ta’addan, Munzur Ya Audu a yankin Arewa-maso-Gabas a wani samame da sojoji suka kai.

Manjo Janar Edward Buba ya ce sojojin sun ƙwato makamai daban-daban guda 145 da alburusai kala-kala har 3,825.

Ya ƙara da cewa sojoji suna yin ƙoƙari sosai domin wargaza ƙarfin ƴan ta’adda tare da lalata hanyoyin ta'addancinsu.

"Sojoji suna kai hare-hare kan sansanonin ƴan ta'adda da sauran wuraren da ke da alaka da ƙungiyoyin ta'addanci."

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun farmaki sansanin sojoji, sun hallaka jami'ai masu yawa

- Manjo Janar Edward Buba

Sojoji sun farmaki ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta samu nasarar kai hare-hare kan ƴan bindiga a jihar Zamfara.

Hare-haren da aka kai ta sama a ƙauyen Babban Kauye da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, ya yi nasarar kashe ƴan bindiga da dama tare da lalata maɓoyarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng