Zanga Zanga Ta Barke a Majalisar Tarayya, Matasa Sun Turawa Tinubu Manyan Bukatu
- Kungiyoyin fararen hula sun mamaye Majalisar Tarayya domin gudanar da zanga-zanga ta musamman a Abuja
- Kungiyoyin sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da bincike kan badakalar da ake samu a bangaren man
- Har ila yau, matasan sun nuna damuwa kan yadda ake zargin shigo da gurbataccen mai daga ketare da yake zama barazana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Matasa sun durfafi harabar Majalisar Tarayya inda suke zanga-zanga kan shigo da man fetur Najeriya.
Kungiyoyin fararen hula da dama ne suka fara zanga-zangar domin bukatar kawo sauyi kan zargin shigo da gurbataccen mai daga ketare.
Danyen mai: Matasa sun bukaci kaddamar da bincike
Premium Times ta ruwaito cewa kungiyoyin sun bukaci a kaddamar da bincike kan badakalar da ke bangaren mai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyoyin sun tura bukatun ne yayin zanga-zangar a Majalisar Tarayya a yau Alhamis 21 ga watan Nuwambar 2024.
Masu zanga-zangar suna dauke da kwalaye inda suka bukaci bangaren mai ya kasance mai zaman kansa.
Sun kuma bukaci kawo karshen tura biliyoyin kuɗi da Gwamnatin Tarayya ke yi zuwa matatun mai da ba su aiki.
Masu zanga-zanga sun soki kwamitin Majalisar Tarayya
Kakakin masu gudanar da zanga-zangar, Kennedy Tabuko ya koka kan yadda Majalisun guda biyu suka yi shiru kan shigo da gurbataccen mai.
Takubo ya ce duk da kafa kwamiti da suka yi kan lamarin har yanzu babu wani abu na cigaba daga ɓangaren Majalisar.
Har ila yau, Takubo ya ce ya kamata Gwamnatin Tarayya ta tsoma kungiyoyin fararen hula da NLC da sauransu kan lamarin.
Masu zanga-zanga sun bukaci korar Kyari
Kun ji cewa gungun masu zanga-zanga sun durfafi Majalisar Tarayya domin bukatar a kori shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari.
Matasan da ke wakiltar kungiyoyi sun bukaci Bola Tinubu ya gargadi Kyari kan tsare-tsare da za su jefa al'umma cikin kunci.
Hakan na zuwa ne yayin da ake zargin Kyari da kawo tsare-tsare da ke sake jefa yan Najeriya cikin mawuyacin hali da ake ciki.
Asali: Legit.ng