Kashim Shettima Ya Fadi Halin da Tattalin Arziki ke ciki bayan Fara Mulkin Tinubu

Kashim Shettima Ya Fadi Halin da Tattalin Arziki ke ciki bayan Fara Mulkin Tinubu

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta ce yanzu haka tattalin arzikin Najeriya ya fara hawa turbar bunkasa kamar yadda ake so
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci bude kasuwar duniya a Legas
  • Ya ce an samu bunkasar tattalin arzikin cikin gida na GDP, kuma gwamnati na kokarin ganin an samu karuwa a kan haka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana matakin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki bayan fara kaddamar da manufofin Bola Tinubu.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce abubuwa su na kyau matuka, ganin cewa tattalin arziki ya fara dawowa hayyacinsa.

Kashim
Gwamnati ta ce tattalin arzikin GDP ya karu Hoto: @stanleynkwocha
Asali: Twitter

BBC Hausa ta wallafa cewa gwamnati ta fara magance matsalolin da su ka dabaibaye tattalin arzikin da ke jawo matsin rayuwa ga yan kasa.

Kara karanta wannan

'Idan babu Arewa, babu Najeriya,' Tinubu ya ce gwamnati za ta bunkasa rayuwar matasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kashim Shettima: "Tattalin arziki na bunkasa"

Jaridar Leadership ta wallafa cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce tattalin azikin Najeriya na cikin gida da ake kira GDP ya karu.

Sanata Kashim Shettima ya kara da cewa a rubu'in farko na shekarar 2024, tattalin arzikin GDP ya kai 2.98%.

Tattalin arziki: Kashim ya fadi kokarin gwamnati

Gwamnatin tarayya ta ce ana daukar matakan da za su taimaka wajen habaka tattalin arziki ta hanyar saukaka kasuwancin a cikin Najeriya.

Mataimakin shugaban kasa ya ce ana sa ran hakan zai taimaka wajen habaka arzikin kasa, kamar yadda ya ke a cikin manufofin Bola Ahmed Tinubu.

Kashim Shettima ya fadi haka ne lokacin da ya ja tawagar gwamnatin tarraya zuwa bude kasuwar duniya da ke Legas.

"Tinubu ya na gyara tattalin arziki," Kashim

A baya kun ji cewa gwamnatin Bola Tinubu ta ce dabarun da ta zo da su ne su ka taimaka wajen hana tattalin arzikin Najeriya rugurgujewa, biyo bayan yanayin da aka same shi.

Kara karanta wannan

An miƙawa gwamnatin Tinubu buƙatar daukar mataki kan haihuwa barkatai

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa yan kasar nan za su ji dadin halin da kasa za ta shiga na bunkasar tattalin arziki a nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.