'Miyagu Sun yi Ƙawanya ga Arewa,' ACF Ta Buƙaci Koyar da Dabarun Kariya
Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta bukaci koyar da dabarun kare kai saboda fitinar yan bindiga da sauran miyagu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Shugaban kungiyar ACF, Mamman Mike Osuman ya ce akwai bukatar sake nazari domin fuskantar matsalolin Arewa da gaske
Mamman Mike Osuman ya yi tsokaci kan ƙungiyar wasu yan Arewa da Malam Ibrahim Shekarau ke jagoranta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta yi kira kan samar da mafita ga matsalolin Arewa.
Shugaban kungiyar, Mamman Mike Osuman ya ce lokaci ya yi da ya kamata yan Arewa su zauna domin magance matsalolin yankinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaban ya yi bayani ne yayin wani taron kungiyar a yau Laraba.
ACF: 'Matsalar tsaro ta yi yawa a Arewa'
Shugaban kungiyar ACF, Mamman Mike Osuman ya ce a halin yanzu ana cikin tsaka mai wuya a Arewacin Najeriya kuma akwai bukatar koyon dabarun kare kai.
Shugaban ya ce matsalar tsaro ta mamaye yankin Arewa kuma lamarin zai iya shafar Najeriya baki daya.
Daily Post ta wallafa cewa Mamman Mike Osuman ya ce lokaci ya yi da dukkan yan Arewa za su hada kai domin magance matsalolinsu.
"A halin yanzu yan bindiga, yan ta'adda, masu garkuwa da mutane da rashin adalci sun yi ƙawanya ga Arewa.
Ya zama wajibi mu zauna domin magance matsalolin tsaro da suka addabe mu.
Dole Sarakuna, yan majalisu da sauran yan siyasarmu su zauna domin magance matsalar da ke kokarin gamawa da yankinmu."
- Kungiyar ACF
Mamman Mike Osuman ya yabi wani kokari da Sanata Ibrahim Shekarau ya fara wajen hada kan shugabannin Arewa.
Sai dai ya ce duk da kokarin da Sanata Shekarau ya fara, akwai buƙatar su yi karatun ta nitsu domin samar da mafita mai dorewa.
Ana fama da talauci a Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin jihohin Arewa sun ce talauci ya fi ƙamari a shiyyar nan idan aka kwatanta da jihohin da ke Kudu.
Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, kuma shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ne ya bayyana haka a taronsu a Kaduna.
Asali: Legit.ng