Sufetan Yan Sanda Ya Shigar da Sanata Kotu kan Badalakar Miliyoyi, an Samu Bayanai

Sufetan Yan Sanda Ya Shigar da Sanata Kotu kan Badalakar Miliyoyi, an Samu Bayanai

  • Ana zargin tsohon sanatan Anambra ta Kudu, Andy Ubah da damfarar makudan kudi har N400m kan ba da mukami
  • Babban Sufetan yan sanda, Kayode Egbetokun ya maka Ubah da wata Hajiya Fatima kan zargin damfarar wani mai suna George Uboh
  • Ubah ya damfari Uboh ne bayan ya yi masa alkawarin muƙamin shugaban hukumar NDDC kan makudan kudi har N400m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babban Sufetan yan sanda, Kayode Egbetokun ya maka tsohon sanata a kotu kan zargin badakala da damfarar miliyoyi.

Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ita ta ba Egbetokun damar daukar mataki kan Sanata Andy Ubah game da zargin damfarar N400m.

Ana zargin tsohon Sanata da damfarar N400m
Sufetan yan sanda maka Sanata Andy Ubah a kotu kan zargin damfarar N400m. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

Ana zargin sanata da damfarar N400m a Najeriya

Vanguard ta ruwaito cewa Egbetokun ya zargi Sanatan da wata Hajiya Fatima wacce yanzu ba a san inda take ba da damfara a 2022.

Kara karanta wannan

Abba Hikima ya jagoranci maka Wike a kotu kan wulakanta yan Arewa a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin sun damfari wani mai suna George Uboh wanda ya yi korafi zuwa ga rundunar yan sanda game da damfararsa da aka yi.

Uboh ya ce Sanata Ubah da abokansa huldarsa sun fada masa cewa suna hanyar samawa mutum shugaban hukumar raya yankin Neja Delta kan kudi N400m.

Sanata Ubah ya karkatar da kudin damfarar

Dan sanda mai gabatar da kara ya ce wadanda ake zargin sun tabbatar da cewa bayanan da suka yi kan aikin ba gaskiya ba ne.

Ya ce hakan ya saba dokar kasa sashe na takwas da kuma sashe na 1 (3) a kundin laifuffuka da hukunci, cewar rahoton TheCable.

An tabbatar da Sanata Ubah da abokansa sun yi nasarar samun kudin inda suka yi amfani da su a karan kansu.

Kashim Shettima ya yiwa Sanata Ubah bankwana

Kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya halarci bikin bankwana da gawar marigayi Sanata da ya rasu.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba da yan sanda suka harbi hadimin gwamna, an samu bayanai

An kawo gawar Sanata Ifeanyi Ubah cikin Majalisar Dattawa domin sanatoci su yi masa bankwana a birnin Abuja.

Wannan na zuwa ne bayan mutuwar Sanata Ubah da ke wakiltar Anambra ta Kudu a Burtaniya a ranar 27 ga watan Yulin 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.