Kano: Malamar da Ta Haura Shekaru 20 Ta na Haura Rafi domin Da'awa Ta Fara Samun Tagomashi

Kano: Malamar da Ta Haura Shekaru 20 Ta na Haura Rafi domin Da'awa Ta Fara Samun Tagomashi

  • Wata baiwar Allah a Kano ta ja hankalin jama'a bayan an gano yadda ta rika koyar da mata ilimin addini a wani kauye kyauta
  • Matar da ke zaune Goron Dutse a cikin Kano ta bayyana yadda ta ke haura wani rafi na tsawon shekaru domin taimakon matan
  • Malama Khadija Muhd, wacce aka fi sani da Malama Jummai ta shaidawa Legit cewa jama'a sun fara kiranta domin ba ta tallafi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Wata malama mai koyar da ilimin addinin musulunci a wani kauye da ke Kano, Khadija Muhammad ta samu yabo daga jama'a kan sadaukar da kanta.

Matar ta shafe akalla shekaru 21 ta na haura wani rafi domin shiga wani tsukukun kauye mai suna Dan Shaye a karamar hukumar Rimin Gado.

Kara karanta wannan

Abba Hikima ya jagoranci maka Wike a kotu kan wulakanta yan Arewa a Abuja

Malama
Malama Khadija ta haura shekara 21 ta na tsallaka rafi don koyar da addini Hoto; Kabiru Bello Tukur
Asali: UGC

Binciken wani gidan rediyo a Kano ne ya gano matar a lokacin da ta ke shirin haura ruwa domin koyar da matan aure ilimin addinin musulunci kyauta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Mata na samun ilimin addini kyauta

Kauyen Dan Shaye a karamar hukumar Rimin Gado a Kano ba sananne ba ne, wanda ba zai rasa nasaba da irin rashin makarantu da asibitoci a kauyen ba.

Amma Malama Khadija Muhammad ta tabbatarwa Legit cewa hakan bai hana ta kai wa matan garin dauki ta hanyar koyar da ilimin addini ba.

Yadda malama ta fara shiga kauyen Kano

Malama Khadija ta bayyana yadda ta fara zuwa kauyen Dan Shayi domin taimakawa matan aure da ilimin addini, ganin yadda hukumomi su ka mata da su.

Ta ce wata kawarta yar asalin garin ce ta nemi taimakonta wajen koyar da mata dokokin addinin musulunci wanda zai inganta rayuwarsu.

Kano: An fara sakawa malama da tagomashi

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano na shirin cika alkawari, an fara runtumo gagarumin aiki a bangaren ilimi

Jama'ar Kano sun fara nuna godiyarsu ga matar da ta sadaukar da lokacinta wajen koyar da matan aure ilimin addini ba tare da neman a biya ta wasu makudan kudi ba.

Dan jaridar da wasu ke mika tallafin ta hannunsa, Kabiru Bello Tukur ya shaidawa Legit cewa yanzu haka kungiyoyi da dama sun fara neman ba Malamar tallafi.

Kabiru Bello Tukur ya ce;

"Akwai mutumin da ya dauki nauyin ba ta dan wani abu na kudin mota duk wata, tun da ta na kashe N2000 a zuwa da dawowa daga garin."

Ita kuma Malama Khadija Muhd, ta shaida cewa akwai wanda ya dauki alkawarin biyansu N30,000 duk wata, wanda ke nufin kowacce daga malaman da ke zuwa za su samu N10,000.

Rahotanni sun bayyana cewa hankalin gwamnatin Kano ya kai kan Dan Shaye, inda ta bayar da umarnin fara gina makarantar Sakandare a kauyen.

Gwamnatin Kano ta dauki mataki kan ilimi

Kara karanta wannan

Kano: Yan sanda sun yi ram da wanda ya zargi kwamishinan Jigawa da zina da matarsa

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta fara daukar mataki a bangaren ilimi watanni shida baya ta ayyana dokar ta baci a sashen saboda tabarbarewarsa.

Kwamishinan ilimi na jihar, Umar Haruna Doguwa ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa gwamnati ta fara gina sababbin ajujuwa 1000 a fadin kananan hukumomi 44 da ake da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.