'Tsaro a Makarantu': Tinubu Zai Kashe N112bn a Gagarumin Aiki da Ya Tattago

'Tsaro a Makarantu': Tinubu Zai Kashe N112bn a Gagarumin Aiki da Ya Tattago

  • Gwamnatin tarayya ta ware N112bn a karkashin shirin samar da kudaden kula da tsaron makarantu domin inganta muhallan koyo
  • Za a kashe kudin ne wajen tabbatar da cewa makarantu sun samu tsaro ga yaran da ke koyon karatu a shekaru uku masu zuwa
  • Imaan Suleiman-Ibrahim ta ce gwamnati ta cimma nasarori wajen kare hakkin yara tun bayan amincewa da dokar hakkokin yara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin shirin samar da kudaden kula da makarantu 'Masu Aminci' za ta kashe N112bn a wani bangare na kokarin kare muhallan koyo.

Ministar harkokin mata, Imaan Suleiman-Ibrahim, ta bayyana cewa wannan shiri zai tabbatar da tsaron makarantu a faɗin Najeriya cikin shekaru uku masu zuwa.

Gwamantin Tinubu ta yi magana kan kashe N112bn wajen samar da tsaro a makarantu
Gwamnatin tarayya ta ware N112bn domin tallafawa shirin samar da tsaro a makarantu. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Tinubu zai kashe N112bn a tsaron makarantu

Imaan Suleiman-Ibrahim ta jaddada cewa gwamnatin tana samun cigaba wajen inganta rayuwar yara ta hanyar shirye-shirye masu amfani, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano na shirin cika alkawari, an fara runtumo gagarumin aiki a bangaren ilimi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministar ta bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin bikin 'Ranar Yara ta Duniya', mai taken “inganta haƙƙin Yara domin ci gaba mai dorewa.”

Ta bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ware N112bn domin tabbatar da cewa makarantu sun samu tsaro domin kwanciyar hankalin kowane yaro.

Minista ta fado dokokin kare haƙƙoƙin yara

Ministar ta bayyana cewa dukkanin jihohi 36 na Najeriya sun amince da 'Dokar Haƙƙin Yara', wadda ta ƙarfafa kariya ga haƙƙoƙin yara da inganta rayuwarsu.

Premium Times ta rahoto Imaan Suleiman-Ibrahim ta lura cewa aiwatar da 'Dokar Hana Cutar da Mutane' ya ƙara ƙarfafa matakan kare yara daga cin zarafi da tashin hankali.

Ta kuma shaida cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na da niyyar tabbatar da cewa kowane yaro yana da damar samun ilimi, kiwon lafiya, da kuma rayuwa cikin tsaro.

Gwamna ya ayyana ilimi kyauta

Kara karanta wannan

'Yadda Bola Tinubu ke aiki tukuru domin ceto ƴan Najeriya daga ƙangin talauci'

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya sanar da ayyana ilimin firamare da sakandare kyauta daga Janairun 2025 domin bunkasa ilimi.

Gwamnan ya ce shirin ba da ilimi kyautan ya dace da dokar 'Haƙƙin Yara ta jihar Abia ta 2006', wadda ke tabbatar da aniyar gwamnati na ganin kowane yaro ya yi karatu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.