Abba Hikima Ya Jagoranci Maka Wike a Kotu kan Wulakanta Yan Arewa a Abuja

Abba Hikima Ya Jagoranci Maka Wike a Kotu kan Wulakanta Yan Arewa a Abuja

  • Barista Abba Hikima, babban lauyan nan mazaunin Kano da ke fafutukar kare hakkin dan Adam ya gano cin fuskar da ake yi wa yan Arewa
  • Ya fadi haka ne bayan ikirarin da ya yi na cewa jami'an tsaro na azabtar da 'yan Arewa da sauran masu kananan sana'o'i a Abuja
  • Ya ce an riga an shigar da kara, kuma ana jiran babbar kotun ta sanya ranar fara sauraren shari'ar domin fara zama kan koken

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Fitaccem lauya, kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Barista Abba Hikima ya jagoranci maka Ministan Abuja, Nyesom Wike a gaban kotu.

Abba Hikima ya kara da cewa haka kuma sun hada da gwamnatin Tinubu da Sufeton yan sandan kasar nan, karar da su ka shigar babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Kara karanta wannan

"Jama'a shaida ne:" Gwamnatin Tinubu ta ce ana fattakar 'yan ta'addan Lakurawa

Hikima
Abba Hikima ya shigar da Nyesom Wike kotu Hoto: Abba Hikima
Asali: Facebook

A bidiyon da Abba Hikima wallafa a shafin Facebook, wanda ya dauka daga gaban babbar kotun tarayya, ya bayyana dalilin shigar korafi kan hukumomin Abuja da na gwamnatin tarayya a gaban kotun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Hikima ya maka Wike a kotu

Bidiyon Abba Hikima ya yi bayanin cewa jami'an 'yan sanda da sauran jami'an hukumar gudanarwar Abuja su na cin zarafin 'yan Arewa da ke ci rani a Abuja.

Ya ce da idanunsa ya ga irin cin mutuncin da ake yi wa wasu daga cikin masu kananan sana'o'i da marasa gata da ke neman mafaka a babban birnin a Lahadin da ta gabata.

Abba Hikima na neman a takawa Wike burki

Barista Abba Hikima ya zargi Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayar da umarnin da ya ci karo da dokar kasa na cewa kowa ya na da 'yancin ya shiga ko ina ba tare da tsangwama ba.

A cewar Abba Hikima:

Kara karanta wannan

"Mu na barin gidajenmu don tsira da rai:" Rashin tsaro ya addabi mazauna Kaduna

"Amma sakamakon wani umarni da Wike, shi ne Ministan FCT ya ba da ran 22 ga Oktoba na cewa duka mabarata su bar Abuja, domin a fadarsa masu zuwa bara su na bata Abuja."

Barista Hikima ya ce ba sa goyon bara, amma jami'an sun yi amfani da damar wajen kama masu kananan sana'o'i tare da karbar cin hanci tare da azabtar da jama'a.

Abba Hikima ya ce an saba doka

A baya mun ruwaito cewa fitaccen lauyan nan da ya goyi bayan gwamnatin Kano gabanin a zabe ta, Abba Hikima ya gano wasu kura-kurai da gwamna Abba Kabir Yusuf ya aikata.

A tsokacin da ya yi kan sake nade Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano, ya ce gwamnati ba ta da wani madagira ta fuskar shari'a na dawo da shi kan karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.