Dubun Wani Ɗan Sandan Bogi Ta Cika a Kano, Kwamishina Ya Aika Sakon Gargadi
- Rundunar 'yan sandan Kano ta samu nasarar cafke wani Hamisu Ibrahim da ke sanya kakin 'yan sanda yana karbar kudin jama'a
- Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna, ya ce wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa yana aiki a wata kotu da ke Ungogo, jihar Kano
- Sanarwar ta ce wasu mutane sun gabatar da koke kan dan sandan bogin inda suka ce ya karbi kudade a hannunsu da sunan taimako
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wani dan sandan bogi da ke ikirarin cewa an turasa aiki a wata kotu da ke karamar hukumar Ungogo.
Bayan samun wani rahoto, kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Salman Dogo Garba, ya ba da umarnin a bincika lamarin tare da kama wanda ake zargin.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da kamen a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 19 ga watan Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An cafke dan sandan boge a Kano
SP Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa wanda ake zargin ya yi amfani da kakakin 'yan sandan yana karɓar kuɗi daga hannun jama'a.
Sanarwar ta ce an kama wanda ake zargi, Hamisu Ibrahim, mai shekaru 42, ɗan kauyen Jangaru da ke karamar hukumar Ungogo, bisa umarnin kwamishinan.
"Bincike ya nuna cewa Ibrahim ya riƙa gabatar da kansa a matsayin ɗan sanda da ke aiki a kotu, yana karɓar kuɗi daga hannun jama’a.
"Mutane biyu sun tabbatar da cewa wanda ake zargin ya karɓi kuɗi daga gare su, da sunan yana taimakawa wajen karbar belin ‘yan uwansu."
- A cewar sanarwar.
Kwamishina ya gargadi masu sojan gona
Sanarwar ta ce kwamishinan 'yan sandan, CP Salman Dogo ya gargadi al'ummar jihar Kano da su kauracewa ayyukan sojan gona da na ta'addanci a jihar.
CP Salman ya ba da tabbacin cewa duk wanda aka samu labarin cewa yana sojan gona da 'yan sanda zai dandani kudarsa idan aka kamashi.
Ya kuma bukaci al'ummar jihar da su rika kai rahoton duk wani motsin da basu yarda da shi ba ko wani da ke sojan gona da rundunar ga ofishin 'yan sanda mafi kusa.
'Yan sanda sun kama sojojin boge
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wasu sojojin boge biyu bisa zarginsu da yin barazanar kashe wani mutum da wuka.
Rundunar ta cafke wani Ben Okafor, wanda ya yi ikirarin cewa shi kofur ne a rundunar sojoji, tare da wani Darlinton Ihenacho a titin Aina, unguwar Isolo a Legas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng