Tinubu Zai Karbo Sabon Bashin Naira Tiriliyan 1.7, Ya Fadawa Majalisa Dalilinsa

Tinubu Zai Karbo Sabon Bashin Naira Tiriliyan 1.7, Ya Fadawa Majalisa Dalilinsa

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya aika sako ga majalisar tarayya ya na neman amincewarta a kan kudurinsa na karbo bashi
  • Shugaban ya ce yana so ya karbo bashin kasar waje na Naira tiriliyan 1.767 domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2024
  • Bukatar Tinubu na zuwa ne yayin da ofishin DMO ya ce bashin waje da ake bin jihohi da tarayya ya karu zuwa $4.89bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya nemi amincewar majalisar tarayya domin ya karbo sabon bashin Naira tiriliyan 1.767 daga kasashen waje.

Idan har majalisar ta amince da wannan bukatar, Shugaba Bola Tinubu ya ce zai yi amfani da kudin wajen cike gibin kasafin 2024 na Naira tiriliyan 9.7.

Shugaba Bola Tinubu ya aika sako ga majalisa na neman amimncewar karbo bashin N1.7trn
Majalisar tarayya ta karanta sakon Tinubu na neman amincewar karbo bashin N1.7trn. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Tinubu zai karbo sabon rancen N1.7trn

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi dalilin Najeriya na shiga sabuwar kungiyar kawancen kasashen duniya

Rahoton Channels TV ya nuna cewa an karanta wasikar da shugaban kasar ya aika a zaman majalisar na ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wasikar, shugaban kasar ya bayyana cewa karbo rancen Naira tiriliyan 1.767 din yana cikin shirin karbo rancen waje da ke a dokar kasafin 2024.

Hakazalika, shugaban kasar ya gabatarwa majalisar rahoton tsarin kasafin 2025-2027 na MTEF/FSP da kuma kuma dokar kafa tsarin zuba jari na kasa.

Idan majalisar ta amice da wadannan bukatu, hakan zai sa tsarin zuba jarin ya zamo ginshikin da za a rika dora dukkanin shirye-shiryen bunkasa al'umma na tarayya.

Bashin da ake bin Najeriya ya karu

Shugaba Tinubu na son karbo wannan bashin ne yayin da bankin CBN ya ce gwamnatin tarayya ta kashe dala biliyan 3.58 wajen biyan basussukan waje a watanni tara na 2024.

A cewar rahoton, bashin da ake bin jihohi 36 na Najeriya ya karu zuwa Naira tiriliyan 11.47 zuwa watan Yunin 2024, duk da karin kudin da suka samu daga asusun FAAC.

Kara karanta wannan

Haraji: Bayan barazanar gwamnoni, majalisa ta yi magana kan buƙatar Tinubu

Wani rahoto da ofishin kula da basussukan Najeriya (DMO) ya fitar ya nuna cewa bashin kasashen waje da ake bin jihohi da gwamnatin tarayya ya karu zuwa dala biliyan 4.89.

Tnubu zai karbo bashin N4.2trn

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya karbo sabon bashin Naira tiriliyan 4.199 (dala biliyan $2.2).

Ministan Kudi, Wale Edun, wanda ya bayyana hakan bayan taron FEC da Shugaba Tinubu ya jagoranta ya ce za a yi amfani da kudin wajen bunkasa tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.