'Kowa Ya Shirya': Malami Ya Hango Gagarumar Matsala da Ke Tunkaro Najeriya a 2025
- Primate Elijah Ayodele wanda ya kafa Cocin INRI Spiritual Evangelical, ya hango hauhawar farashi mai tsanani a 2025
- Ya ce hauhawar farashi a yanzu ba komai ba ne idan aka kwatanta da abin da ke tafe, yana kira ga gwamnati ta dauki mataki
- Ayodele ya kuma yi hasashen cewa farashin makamashi zai yi tsada a 2025, inda ya bukaci gwamnati ta rage radadi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Fitaccen malamin addinin Kirista, Primate Elijah Ayodele ya hango matsananciyar tsadar rayuwar da ke jiran 'yan Najeriya a shekarar 2025.
Primate Ayodele wanda shi ne shugaban cocin INRI Spiritual Evangelical ya ce Najeriya za ta fuskanci hauhawar farashin kayayyaki mai tsanani a badi.
Kamar yadda rahoton Business Africa ya nuna, malamin ya sanar da hasashensa ne a ranar Lahadi, 17 ga Nuwambar 2024 a cikin cocinsa da ke Legas
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin coci ya hango tsadar rayuwa a 2025
Malamin ya ce hauhawar farashin da ake gani a wannan shekarar tamkar 'wasan yara' ne, za a fuskanci asalin tsadar rayuwar ne a shekarar 2025.
Primate Ayodele ya bukaci gwamnati da ta dauki matakan da za su rage tsadar kayan masarufi ta yadda al'umma za su samu saukin wahalhalun da suke ciki.
Malamin ya bayyana cewa za a fuskanci tsadar makamashi a shekara mai zuwa inda ya ce mutane za su azabtu da tsadar makamashin.
'Makamashi zai yi tsada a badi' - Fasto Ayodele
Da wannan ya ki kira ga hukumomin da abin ya shafa da su dauki matakan kariya tun yanzu na hana farashin makamashi tashi.
Primate Ayodele ya ce:
"Muna bukatar dagewa da addu'a saboda za a fuskanci matsananciyar hauhawar farashin kayayyaki a shekara mai zuwa. Tsadar rayuwa za ta mamaye tattalin kasar.
Hakazalika, makamashi zai zo ya yi tsada ta yadda mutane za su shiga matsanancin yanayi saboda tsadar. Ya zama wajibi gwamnati ta dauki matakai."
Farashin wasu kayan abinci a Kaduna
A yayin da Fasto Ayodele ya yi wannan ikirari, Legit Hausa ta tambayo farashin da ake sayar da kayana abinci a wasu yankunan Kaduna.
Al'ameen Muhammed, dan kasuwa a Kasuwar Bacci, ya ce shinkafa 'yar kamfanin Gerawa da aka fi saye yanzu ta koma N83,500 inda a watan baya ta ke ksa da N70,000.
Lita hudu ta jarkar manja ta komai N0,500 (sabon kamfani) amma lita biyar a babban kamfani kamar Turkey ya kai N19,500 yayin da mangyada ya kulle N20,000 da doriya.
A cewarsa, mudun sukari a yanzu ya kai N3,000 inda katan din taliya mai kwabo yake a N20,500.
'Tinubu ya jawo tsadar rayuwa' - Dan majalisa
A wani labarin, mun ruwaito cewa Hon. Nnamdi Nzechi ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kama Bola Tinubu da laifi kan tsadar rayuwar da ake ciki a kasar nan.
Hon. Nzechi wanda ke wakiltar mazabar Ndokwa/Ukwani da ke jihar Delta a majalisar wakilai ta tarayya ya ce manufofin Tinubu sun jefa 'yan Najeriya cikin wahala.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng