Abu Ya Faskara: Dangote Na Neman Bashin Biliyoyin Daloli domin Shigo da Danyen Mai
- Attajirin dan kasuwar nan na Najeriya, Aliko Dangote, na neman tara biliyoyin daloli domin shigo da danyen mai daga waje
- Rahoto ya ce Dangote ya fara tuntubar wasu bankunan kasa da kasa, kamfanoni da sauransu domin samun rancen kudaden
- Wannan dai na daga cikin yunkurin da Dangote ke yi na ganin matatar mansa na iya tace ganga 650,000 a kowacce rana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya fara tattaunawa da wasu bankunan kasashen waje domin samun jarin biliyoyin daloli na shigo da danyen mai.
Kamfanin hada-hadar kudi na Afirka (AFC), mai ba da lamuni na ci gaban Afirka na daya daga cikin cibiyoyin da ke cikin tattaunawar neman rancen kudin.
Dangote na neman kudin shigo da mai
Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa matatar Dangote na bukatar sayen karin danyen mai domin ta rika tace ganga 650,000 a kowacce rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tuni, kungiyar KSG, gungun kwararru daga Amurka da Birtaniya da ke ba da bayanan sirri na kasashe, sun ce matatar za ta iya cimma karfinta a shekarar 2025.
"Idan har matatar ta cimma karfinta na tace danyen man, to za a samu rangwamen farashin mai a kasuwannin gida kuma zai jawo abokan ciniki daga Turai."
“KSG ta yi la’akari da cewa sauye-sauyen da Najeriya ta yi na dogaro da man da aka tace a cikin gida zai iya baiwa kasashen Turai damar rage dogaro da sayen mai daga Rasha."
- A cewar rahoton.
KSG ta hango raguwar farashin fetur
Rahoton Financial Times, ya nuna cewa KSG ta hango raguwar farashin mai a Najeriya da zarar matatar Dangote ta kai ga koluluwar aikinta, kuma zai jawo gasa a kasuwannin Turai.
"Gazawar gwamnati wajen magance matsalolin matatun man na iya haifar da tarzomar siyasa gami da zanga-zanga, yayin da cire tallafin man fetur ke kara ta’azzara rikicin."
- A cewar kungiyar KSG.
Neman kudaden da Dangote ke yi na nuni da cewa danyen mai da NNPPC ke hakowa a Najeriya ba zai iya wadatar da bukatar matatar Dangoten ba.
'An daina shigo da fetur' - NNPCL
A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari ya ce sun daina shigo da tataccen man fetur daga ketare.
Mele Kyari ya ce bai kamata 'yan Najeriya su yiwa NNPCL ca a kan abin da suka riga da sanin amfaninsa ba, yana mai cewa kamfanin ba ya adawa da matatar Dangote.s
Asali: Legit.ng