An gina daular kasuwancin Aliko Dangote ne daga rancen da ya karba daga kawunsa

An gina daular kasuwancin Aliko Dangote ne daga rancen da ya karba daga kawunsa

Aliko Dangote dan kasuwa ne da ya tsallaka gaɓar tekun nahiyar Afirka. Dayawa sun fahimci cewa hamshakin attajirin dan kasuwar kuma mai taimakon jama'a shine yafi kowa kudi a Afirka, amma ba kowa ya san yadda ya samu kudin sa ba.

A kan haka ne, Legit ta lissafo kasuwancin Dangote guda hudu da yadda mutumin mafi arziki a Afirka ya fara daular sa ta hanyar karbar bashi daga wajen kawunsa.

KU KARANTA KUMA: Yana da matukar wuya a siyar da gurbataccen kaya, Baba-Ahmed ya yi wa Garba Shehu ba’a a shirin talbijin

Rayuwa a Kano

Kakan Aliko Dangote, Sanusi Dantata, ya zama waliyyinsa bayan ya rasa mahaifinsa a shekarar 1965. Ya koyi abubuwa da yawa daga wannan mai kula da shin yayin da yake tasowa.

Sha'awar Dangote a harkar kasuwanci ta faro ne tun lokacin yarintarsa lokacin da zai sayi kwalayen alawa sannan kuma ya fara siyarwa kawai don ya samu riba.

An gina daular kasuwancin Aliko Dangote ne daga rancen da ya karba daga kawunsa
An gina daular kasuwancin Aliko Dangote ne daga rancen da ya karba daga kawunsa Hoto: Wei Leng Tay/Bloomberg
Asali: Getty Images

Ya karɓi rance daga kawunsa don gina daularsa

Bayan ya kammala karatunsa na jami'a a 1977, Dangote ya karbi rancen $ 3,000 (N1,143,000 kamar yadda yake a halin yanzu) daga kawunsa don fara kasuwanci.

Yana shigo da shinkafa daga kasar Thailand da sukari daga kasar Brazil wanda ya ke sayarwa masu amfani a ƙauyensa.

A cewar dan kasuwar, a ranakun da ya taki sa’a, yana samun ribar dala 10,000 a kowace rana (N3,810,000 kamar yadda yake a halin yanzu). Hakan ya bashi damar biyan bashin kawun nasa cikin watanni uku kacal.

Attajirin ya sami damar juya kasuwancin sa zuwa daular biliyoyin dala lokacin da ya dakatar da shigo da kaya daga waje sannan ya fara samar da abin da yake shigowa da shi.

Dukiyarsa ta ba shi damar taimakawa al’umma kasancewar yana ɗaya dagga cikin masu manyan ma'aikatu a Afirka.

KU KARANTA KUMA: Hotunan babur mai doguwar kujerar da ka iya daukar mutum 8 ta haddasa cece-kuce

Kasuwancin sa guda huɗu

Rukunnan masana'antun sa sun hada da: Dangote Sugar Refinery PLC., National Salt Company of Nigeria PLC., Dangote Flour Mills PLC., da Dangote Cements PLC.

A baya mun ji cewa Aliko Dangote shine mutumin da ya fi kowa kudi a Nahiyar Afrika wanda ya mallaki dala biliyan $ 12.1 (N4,608,527,000,000).

Mutumin mai shekaru 63 ya samar da kamfanin kera siminti mafi girma a Afirka wanda ake kira Dangote Cement.

Attajirin kuma mai aikin taimako yana da matatar mai da aka fara aikinta tun shekarar 2016 kuma ana sa ran zata kasance daya daga cikin manyan matatun mai a duniya da zarar an kammala ta.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel