Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Bama Bamai kan 'Yan Bindiga, an Sheke Miyagu Masu Yawa
- Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun samu nasarar kai hare-hare kan ƴan bindiga a jihar Zamfara
- Gwarazan sojojin sun yi ruwan wuta kan ƴan bindiga a ƙauyen Babban Kauye na ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar
- Hare-haren na sama da aka kai kan ƴan bindigan masu shirin kai hari ga sojoji, sun yi sanadiyyar hallaka miyagu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta samu nasarar kai hare-hare kan ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Hare-haren da aka kai ta sama a ƙauyen Babban Kauye da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, ya yi nasarar kashe ƴan bindiga da dama tare da lalata maɓoyarsu.
Rundunar sojoji ta farmaki ƴan bindiga
Daraktan hulɗa da jama'a da yaɗa labarai na NAF, Olusola Akinboyewa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa hare-haren waɗanda aka kai a ranar 15 ga Nuwamba, wani ɓangare ne na aikin rundunar Operation Fansan Yamma, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Akinboyewa ya ce an kai harin ne bisa bayanan sirri da ke nuna cewa ƴan bindiga na shirin kai hare-hare kan fararen hula da jami’an sojoji da ke yankin Tsafe.
Sojojin sama sun sheƙe ƴan bindiga
Ya ƙara da cewa harin bam ɗin ya yi sanadiyyar mutuwar miyagu masu yawa da suka haɗa da manyan makusantan shugabannin ƴan bindiga Dan-Isuhu da Dogo Sule.
"Waɗannan hare-hare ta sama an kai su ne kan wani gagarumin taron ƴan bindiga a ƙauyen Babban Kauye da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara."
"Rahotanni sun tabbatar da cewa an kawar da wasu manyan mambobin ƙungiyoyin ƴan bindigan, lamarin da ya raunana ƙarfin su."
- Olusola Akinboyewa
Akinboyewa ya ƙara da cewa sojoji sun ƙudiri aniyar tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma samar da tsaro a ƙasar nan.
Sojoji sun ragargaji ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojin sama na rundunar Operation Fansan Yamma sun ragargaji ƴan bindiga a jihar Kaduna.
Dakarun sojojin saman sun tarwatsa wata babbar maɓoyar ƴan bindiga da ke tsaunin Dunya da dajin Batauna a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng