Injiniya Ya Nuna Shakku kan Dalilin Yawan Lalacewar Layin Wutar Lantarki
- A watan Nuwamban nan TCN ya fitar da sanarwa cewa wasu sun yi barna, sun lalata layin wutar Lokoja-Gwagwalada
- Kamfanin ya ce an dade ana aika-aika, ana barin mutane suna cigaba da zama cikin duhu a wasu jihohin Najeriya
- Wani Injiniya, Yusuf Tahir Adamu bai ganin barayi ne suke satar na’urorin, ya na ganin akwai abin da ba a sani ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Kamfanin TCN ya shaidawa duniya cewa an samu miyagu da suka yi ta’adi a layin wutar lantarkin Lokoja-Gwagwalada.
Abin ya faru ne a lokacin da al’umma musamman a yankin Arewacin Najeriya ke fama da matsananciyar matsalar lantarki.
TCN ta zargi 'yan iska da lalata wuta
Sanarwar da TCN fitar kamar yadda wani Imran Muhammad ya sake wallafawa a X ya nuna mutane ba su gamsu da zancen nasu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ndidi Mbah wanda ita ce jami’ar hulda da jama’a ta kamfanin ta bayyana cewa miyagu sun yi awon gaba da wani karfen aluminum.
Kafin yanzu, TCN ya ce an yi barna a layin Gwagwalada-Kukuwaba-Apo da na Gwagwalda-Katampe duk a cikin shekarar nan.
Injiniya Yusuf Tahir Adamu ya na cikin wadanda suka yi magana a shafin na X, yana mai nuna alamar tambaya kan zancen TCN.
Martanin da aka yi wa kamfanin TCN
Akwai masu ganin babu barayin da za su sace karfen aluminum da yake daukar wutar lantarki domin ba su ma san inda yake ba.
Ko da an sace kuwa, Yusuf ya ce barayi ba za su san inda za su saida karfen a kasuwa ba saboda watakila ba zai yi wahalar ganewa ba.
Ganin girman karfen da ake magana, Injiniya Yusuf Adamu ya ce babu yadda za a iya a dauki abu mai tsawon mita 500 cikin sauki.
Masanin ya ba mahukuntan TCN shawara su yi duba cikin gida a kan zargin miyagu da satar karafunan da ya jefa mutane a duhu.
Injiniya ya yi magana kan satar kayan wuta
"Miyagu sai dai su lalata. Ba za su bukaci su dauki sinki biyu na karfen aluminum ba.
"Ba za mu san inda za su saida shi ba. Tsawon layin 330kc zai iya kai mita 500.
"Kilomitar ACSR ba za ta dauku ba tare da na’ura ba. Kamfanin TCN ya dai duba cikin gida."
- Yusuf Tahir Adamu
Da gangan ake sace kayan wutar lantarki?
Masu tofa albarkacin bakinsu suka ce babu wanda zai iya sace kayan sai wanda ya san kayan wutar lantarki da kuma yadda suke aiki.
Wasu su na ganin da gangan ake wannan danyen aiki domin a fitar da kudi da sunan gyara, akwai kuma masu addu’ar Allah tona asiri.
Za a karawa jihohin wutar lantarki
Labarai sun zo kafin yanzu cewa wasu jihohi za su samu karin hasken wutar lantarki bayan rokon da Abba Kabir Yusuf ya yi wa minista.
Jihohi hudu kamfanin TCN ya ce ya kara yawan hasken da ake tura masu bayan Arewacin kasar nan ya sha fama da duhu na kwanaki.
Asali: Legit.ng