Gwamna Ya Fusata kan Kisan Sojoji a Jiharsa, Ya Fadi Matakin Dauka

Gwamna Ya Fusata kan Kisan Sojoji a Jiharsa, Ya Fadi Matakin Dauka

  • Gwamnan Abia ya nuna takaicinsa kan ɗanyen aikin da ƴan bindiga suka aikata na kashe sojoji a jihar
  • Alex Otti ya nuna alhininsa kan kisan tare da jajantawa rundunar sojojin Najeriya kan rashin jami'an tsaron da aka yi
  • Gwamna Alex Otti ya kuma sha alwashin zai yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa an hukunta masu hannu a harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Gwamna Alex Otti na Abia ya nuna takaicinsa kan kisan da ƴan bindiga suka yi wa sojoji a jihar.

Ƴan bindigan dai sun hallaka sojojin ne bayan sun kai musu hari a shingen bincikensu.

Otti ya fusata kan kisan sojoji a Abia
Gwamna Otti ya fusata kan kisan da 'yan bindiga suka yi wa sojoji a Abia Hoto: Alex C. Otti
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa Gwamna Otti ya aika da wasiƙar jaje ga muƙaddashin hafsan sojojin ƙasa (COAS), Laftanar Janar Olugemi Oluyede.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Gwamna Otti ya ce kan kisan sojoji

Kara karanta wannan

An rasa rayuka bayan 'yan bindiga sun farmaki sojoji a wani shingen bincike

Gwamna Otti ya yi wa rundunar sojojin Najeriya jaje bisa wannan ɗanyen aikin da ƴan bindiga suka yi wa jami'anta.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata wannan ta'asar.

"Cike da takaici na rubuto maka wannan wasiƙa domin jajantawa kan kisan rashin tausayi da maharan da ba a san ko su wanene ba suka yi wa sojoji uku a garin Umuopara na ƙaramar hukumar Umuahia ta Kudu a jiha ta."
"Lallai wannan harin na ba gaira ba dalili da aka kai wa sojojin mu da suka jajirce wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar Abia abin Allah wadai ne."
"Ina tabbatar maka cewa gwamnatin jihar Abia ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai an kama waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da hukunta su."
"A shirye gwamnatina take ta haɗa kai da sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro domin gudanar da cikakken bincike domin zaƙulo masu hannu a harin."

Kara karanta wannan

Badakalar N1.3trn: Tsohon gwamna ya yi martani kan gayyatar da EFCC ta yi masa

- Gwamna Alex Otti

Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojin sama na rundunar Operation Fansan Yamma sun ragargaji ƴan bindiga a jihar Kaduna.

Dakarun sojojin saman sun tarwatsa wata babbar maɓoyar ƴan bindiga da ke tsaunin Dunya da dajin Batauna a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng