'Mun Yi Kokarinmu': Malamin Musulunci kan Ragargazar Bello Turji da Sojoji Ke Yi

'Mun Yi Kokarinmu': Malamin Musulunci kan Ragargazar Bello Turji da Sojoji Ke Yi

  • Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya yi magana kan kofar-rago da rundunar sojoji ta yiwa yan ta'adda a Najeriya
  • Sheikh Aliyu ya yi farin ciki kan lamarin inda ya yi addu'ar samun nasara ga sojojin kan yan bindiga a Arewacin Najeriya
  • Malamin ya ce tun da sun yi ta kiran yan ta'adda da Bello Turji su shiryu amma sun ki, suna addu'ar a tarwatsa su da kawo karshensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Malamin Musulunci, Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya yi magana kan ragargazar yan bindiga da sojojin Najeriya ke yi.

Malamin ya ce abin murna ne yadda sojojin Najeriya suka yiwa yan ta'adda kofar-rago inda ya yi fatan nasara ga sojoji.

Malamin Musulunci ya magantu kan artabun sojoji da Bello Turji
Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya yi addu'a ga sojoji kan artabu da Bello Turji. Hoto: Karatuttukan Malaman Sunnah.
Asali: Facebook

Sheikh Aliyu Kaduna ya soki Bello Turji

Kara karanta wannan

Zuwa bikin 'liyafa' da malamai suka yi na auren yar Kwankwaso ya tayar da kura

Sheikh Aliyu Kaduna ya bayyana haka ne a cikin faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Sunnah ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya ce sun yi iya bakin kokarinsu wurin kira ga yan ta'addan da Bello Turji su bar wannan aiki na ta'addanci amma a banza.

"Mun dade muna kira ga Bello Turji da yan ta'adda masu kashe mutane suna garkuwa da su, muna kiransu da karanta musu ayoyin Alkur'ani da hadisai su tuba."
"Komai barnar da ka yi Allah bai rufe maka kofar tuba, kuma ba mai shiga tsakanin Allah da bawa ya ce wane ba za a karbi tubansa ba ko malami ne."

- Ibrahim Aliyu Kaduna

Shehi ya yi addu'a ga sojojin Najeriya

"Labarin da yake zuwa mana a yanzu, sojojin Najeriya sun yi musu kofar-rago kuma Alhamdulillah ana samun nasara a kansu, tun da sun ki jin nasiha, Allah ya kawo karshensu."

Kara karanta wannan

'Babu mai karya ni': Wike ya fusata kan rigimar PDP, ya soki gwamna kan matsalarta

"Allah ya ba jami'an tsaronmu nasara su murkushe su, Allah ka karfafe su ka basu iko su kawo karshen wadannan yan bindiga."

- Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna

Malamin ya yi addu'a Ubangiji ya sa a ji labari mai dadi cewa an kashe Bello Turji saboda cutar da Musulunci da yake yi.

Sheikh Aliyu ya magantu kan halin kunci

Kun ji cewa Malamin addinin Musulunci a jihar Kaduna ya nuna fushi kan yadda aka wayi gari da karin kudin man fetur a fadin Najeriya.

Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya ce karin kudin mai a wannan halin da ake ciki ya nuna akwai rashin tausayi a zuciyar shugabanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.