Bashin Jihar Kano Ya Karu da Dala Miliyan 22 duk da Abba bai Taba Karbo Aron Kudi ba

Bashin Jihar Kano Ya Karu da Dala Miliyan 22 duk da Abba bai Taba Karbo Aron Kudi ba

  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce tun da aka rantsar da ita a 2023, ba ta taba cin bashi a gida ko kasashen waje ba
  • Amma Dr. Abdulrazaq Ibrahim Fagge ya fahimci an samu karin $22,074,008.63 a kan bashin da ake bin jihar Kano
  • Dr. Hamisu Sadi Ali ya ce an samu karin ne a dalilin shigowar wasu bashi da Abdullahi Ganduje ya karbo a 2018

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi ikirarin cewa tun da ta shiga ofis ba ta taba karbo bashin kudi daga gida ko kuwa a waje ba.

Wannan ikirari ya kara tabbatar da da’awar Kwankwasiyya na kyamar karbo aron kudi a bankuna ko manyan hukumomin duniya.

Abba.
Gwamnan Kano ya gujewa cin bashi da ya shiga ofis Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Kwanaki bayan gwamnatin Kano ta ce ba ta taba cin bashi ba, sai Dr. Abdulrazaq Ibrahim Fagge ya yi mata martani a Facebook.

Kara karanta wannan

Najeriya na tangal tangal, Tinubu zai runtumo sabon bashin Naira tiriliyan 4.2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Abdulrazaq Ibrahim Fagge ya karyata maganar da ta fito daga ofishin da ke kula da harkokin bashi, ya gabatar da wasu alkaluma.

Gwamnatin Abba ta karbo bashi a Kano?

Masanin harkar tattalin arzikin ya nuna akwai alamar tambaya game da ikirarin gwamnatin Abba Yusuf domin bashin ya karu.

Dr. Fagge ya ce a Yunin 2023, ana bin gwamnatin Kano bashin $101,319,905.05 a bankunan waje, amma yanzu ya zama $123,393,914.59.

Daga lokacin da Abba ya gaji Abdullahi Ganduje zuwa yanzu, alkaluma sun nuna bashin ketaren da ake bin Kano ya karu da $22,074,008.63.

Gwamnatin Abba ta yi bayanin karuwar bashi

Amma Hamisu Sadi Ali, PhD wanda shi ne shugaban hukumar kula da bashi a Kano ya yi raddi a Facebook, ya ce ba bashi aka karbo ba.

Menene ya jawo karin, sabon bashi aka karbo? Amsar ita ce a’a.
Abin da Dakta ya ki fahimta shi ne ba a aiko da bashin ketare a lokaci guda, masu ba da aron kudi su na yi ne daki-daki.

Kara karanta wannan

EFCC: 'Yadda wani gwamna a Najeriya ya tura miliyoyin Naira zuwa asusun ɗan canji'

- Hamisu Sadi Ali, PhD

Dr. Hamisu Sadi Ali ya ce tsakanin Yunin 2023 zuwa na 2024, an aiko da ragowar bashin aikin ruwan Kano wanda aka ci tun a 2018.

Duk da kudin da ake bin jihar sun karu, Hamisu Ali ya tabbatar ba yanzu aka ci bashin ba, abin da ya faru ne tun a gwamnatin APC.

Abba ya karbo bashi daga kasar Faransa?

Kwanaki aka samu labari cewa gwamnatin Kano ta musanta raɗe-raɗin da ake cewa ta karɓo rancen Naira biliyan 177 daga kasar Faransa.

Darakta Janar na ofishin kula da basussuka, Dr. Hamisu Sadi Ali ya ce Gwamna bai karbo rancen ko sisi ba tun da ya hau mulki a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng