Ribadu na Fitar da Najeriya Kunya: Tsohon Sanata Ya Yaba da Inganta Tsaro

Ribadu na Fitar da Najeriya Kunya: Tsohon Sanata Ya Yaba da Inganta Tsaro

  • Tsohon Sanata, Shehu Sani yaba da yadda mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya jajirce
  • Ya bayyana wasu daga cikin nasarorinsa tare da gaggauta dakatar da ayyukan yan ta'adda da ke lalata wutar lantarki
  • Sanata Shehu Sani ya kwatanta Nuhu Ribadu da magabatansa a ofishin, inda ya zarge su da gaza tabuka komai a kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna, Shehu Sani ya ji dadin yadda ofishin mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro ke gudanar da aikinsa.

Sanata Shehu Sani ya ce ayyukan da ofishin karkashin Nuhu Ribadu ya na ayyukan da ya dace wajen magance rashin tsaro.

Ribadu
Shehu Sani ya yabawa Nuhu Ribadu Hoto: Nuhu Ribadu/Shehu Sani
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Shehu Sani ya ce akwai babban banbanci tsakanin ayyukan Nuhu Ribadu da wadanda su ka gabace shi a ofishin.

Kara karanta wannan

Zargin da shugaban NNPP ya yi wa Sanata Kawu har ake barazanar kai shi kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Sanata ya lissafa nasarar NSA

Sanata Shehu Sani ya bayyana jin dadin yadda ofishin Nuhu Ribadu ya jagoranci kashe manyan yan ta'adda a kasar nan.

Ya kara da cewa Nuhu Ribadu ya yi kokari ainun wajen kakkabe ayyukan yan ta'adda da ke tare jama'a a hanyoyin kasar nan tare da garkuwa da mutane.

Ribadu ya kara da yabon yadda hukumomin tsaron kasar nan su ka gaggauta takawa yan ta'adda masu lalata turakun wuta birki kafin aikinsu ya fi haka muni.

"Nuhu Ribadu ya kere magabatansa:" Tsohon Sanata

Sanata Shehu Sani ya zargi tsofaffin mashawarta shugaban kasa kan harkokin tsaro da gaza tabuka abin a zo a gani a lokacinsu.

Ya bayyana cewa duk da biliyoyin da gwamnati ke kashewa a harkar tsaro, ba su cimma rabin nasarorin da Nuhu Ribadu ya ke samu a yanzu ba.

Tsohon Sanata ya yaba da tsaron Najeriya

A wani labarin kun ji cewa tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna, Shehu Sani ya ce akwai wadansu a kasar nan da ke adawa da yadda ake tafiyar da tsaro cikin nasara kan yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Dan majalisar Kano ya jawo surutu, an hango shi da kudi cike da daki ana matsin rayuwa

Sanata Shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya ya kara da yabon karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle bisa kokarin da ya ke wajen yaki da ta'addanci a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.