Jami’ar Kogi Ta Hukunta Malamai 4 da Ake Zargin Sun Yi Lalata da Dalibai

Jami’ar Kogi Ta Hukunta Malamai 4 da Ake Zargin Sun Yi Lalata da Dalibai

  • Kwamitin gudanarwa na jami’ar tarayya ta Lokoja ya kori malamai hudu kan lalata da dalibai domin kare martabar ilimi
  • Victor Ndoma-Egba wanda ya jagoranci zaman kwamitin, ya yabawa mahukuntan jami’ar kan bin ka’ida yayin binciken
  • Kwamitin ya nemi jami’ar Kogi da ta hanzarta warware sauran shari’o’in cin zarafin dalibai, musamman na sashen kimiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kogi - Kwamitin gudanarwar jami’ar tarayya ta Lokoja (FUL) da ke jihar Kogi ya amince da korar wasu malamai hudu kan zargin lalata da dalibai.

Karkashin jagorancin Victor Ndoma-Egba, kwamitin ya yanke wannan hukunci a taronsa na biyu, domin tabbatar da da'a tsakanin malaman jami’ar.

Kwamitin gudanarwar jami'ar tarayya ta Lokoja, ya kori malamai biyu kan zargin lalata
An sallami malamai biyu daga jami'ar tarayya ta Lokoja kan zargin lalata da dalibai. Hoto: @fulokoja
Asali: Twitter

Lalata: Jami'ar Kogi ta gargadi malamai

Kwamitin ya yabawa shugabannin jami’ar kan gudanar da bincike na adalci, tare da jaddada rashin amincewa da duk wani nau'in cin zarafin dalibai inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Ondo: Kotun ɗaukaka ƙara ta kori ɗan takarar gwamna kwanaki 2 gabanin zaɓe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Victor Ndoma-Egba ya gargadi ma’aikata da malamai kan aikata ba daidai ba, ya kuma bukaci dalibai da su rika kai rahoto ga hukumar makarantar idan an ci zarafinsu.

Kwamitin ya kuma umarci jami’ar da ta gaggauta yanke hukunci kan sauran shari’o’in cin zarafi da ke gabanta, musamman wadanda ke faruwa a sashen kimiyya.

Yadda aka kori malamai saboda lalata

Jaridar The Cable ta rahoto cewa a shekarar 2020, kwamitin gudanarwa na jami’ar Modibbo Adama da ke jihar Adamawa ya kori malamai biyu kan cin zarafin dalibai.

An sallami Yakubu Bobboi da Toma Fulani Mbahi kan zargin yin lalata da wata dalibar digirin digirgir mai suna C. A. Bathon.

Haka kuma, jami’ar Modibbo ta kuma sallami Bakari Girei daga aiki kan almubazzaranci da Naira miliyan 1.1 na jami’ar.

An ragewa farfesoshi 3 mukami a jami'a

A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'ar Modibbo Adama ta jihar Adamawa (MAU) ta rage wa wasu farfesoshi uku mukami saboda samunsu da laifuka masu alaka da lalata.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bayyana gaskiya kan tashin bam a babban birnin jihar Arewa

Jami'ar ta bayyana cewa nan bada dadewa ba za ta aiwatar da dokoki na hukunta laifuffukan lalata tsakanin malamai da dalibai kuma ba za ta dagawa kowa kafa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.