Rikicin addini ya ɓalle tsakanin ɗalibai Musulmai da Kirista a jami’ar Yola

Rikicin addini ya ɓalle tsakanin ɗalibai Musulmai da Kirista a jami’ar Yola

Wani tashin hankali ya auku a jami’ar Modibbo Adama dake garin Yola na jihar Adamawa, biyo bayan rakaddama game da shugabancin dalibai, wanda ya rikida ya koma rikicin addini.

Rariya ta ruwaito wannan rikici da yayi sanadiyyar babbaka daga daga cikin Masallatan dake cikin jami’ar ya faru ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Feburairu, ina baya ga Masallacin, rikicin ya shafi tsangayar ilimin gudanarwa.

KU KARANTA: Jerin muhimman kalmomin hausa 20 da ma'anar su a harshen turanci

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daliban jami’ar sun shiga halin dimuwa da rashin tabbas, inda aka hange kowa na ta kansa, musamman tun bayan da hukumar makarantar ta girke jami’an rundunar Yansanda da ma na rundunar Soji a jami’ar.

Rikicin addini ya ɓalle tsakanin ɗalibai Musulmai da Kirista a jami’ar Yola
Jami'ar Modibbo

Da aka tuntuni kwamishinan Yansandan jihar, Othman Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, sa’annan tuni ya aika da jami’an kwantar da tarzoma don shawo kan hatsaniyar.

Daga karshe Kwamishinan ya tabbatar ba ayi asarar rai ko daya ba, kuma zuwa yanzu hankula sun kwanta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng