Yadda aka Kawo Karshen Yakin Fulani da Berom na Shekaru 35 a Filato
- A jihar Filato, an fara samun zaman lafiya tsakanin kabilun Fulani da Berom da suka shafe shekaru suna fada da juna
- Kungiyar samar da zaman lafiya ta YIAVHA ta shiga ƙauyukan da ake fama da yawan rikici sosai domin sasanta kabilun
- A damuwar bana, an samu hadin kai tsakanin Fulani da Berom inda suka yi noma tare kuma suka hada kai wajen girbe amfanin gona
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato - Kabilun Fulani da Berom sun fara samun fahimtar juna bayan shafe shekaru 35 suna yaki a tsakaninsu.
Kungiyar YIAVHA mai fafutukar samar da zaman lafiya ta shiga ƙauyuka da dama domin fahimtar da kabilun muhimmacin kaucewa rikici.
Jacob Choji Pwakin ya wallafa bidiyon yadda Fulani da Berom suka hada kai wajen aikin gona a damunar bana a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fulani da Berom za su zauna lafiya
An shafe shekaru sama da 35 dan ƙabilar Berom da bai isa ya shiga yankin Fulani ba a wasu yankunan jihar Filato.
Kungiyar YIAVHA ta kutsa ƙauyukan Banghai, Riyan, Kwi, Fass, Jol, Mahanga Ngyelgagare da Rim domin kawar da rikicin da ya dauki shekaru.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa YIAVHA ta yi dabaru wajen hada kan Fulani da Berom wajen yin aikin gona tare.
"Shekara 35 rabo na da zuwa garin Fulani saboda rikici. Bayan samun zaman lafiya, da na je garin Mahanga, kabilata sun yi tsammanin bazan dawo da rai ba."
- Danjuma Daylop, dan kabilar Berom
"A lokacin da aka ce za mu yi noma da Berom na yi tunanin cewa hakan ba zai taba yiwuwa ba."
- Idris Muhammad, Fulani
"Yanzu mun samu hadin kai, na kulla alaka da mutanen Berom ta hanyar nomar haɗaka. Na san sunayensu, ina da lambar wayarsu kuma muna magana sosai."
- Hamza Aminu, Fulani
Jami'ar kungiyar YIAVHA, Judith Remson ta ce sun tattauna da matasa a yankunan a lokacin da suke ƙoƙarin aikin.
Shugaban YIAVHA, Choji Pwakin ya ce akwai buƙatar samar da makarantu, asibitoci da sauransu domin kawo karshen rikicin baki daya.
An yi rikici da makiyaya a Adamawa
A wani rahoton kun ji cewa rikici ya sake ballewa tsakanin manoma da makiyaya a jihar Adamawa, inda rayukan jama'a su ka salwanta.
An yi zargin wasu da ake zargin makiyaya ne sun bi gidajen mazauna Kukta da ke Waltandi da ke karamar Song suka afaka musu.
Asali: Legit.ng