Rikicin Jos: Ba Zan Kashe Mahaifina Ba Saboda Yana Addinin Musulunci, Kakakin Majalisa

Rikicin Jos: Ba Zan Kashe Mahaifina Ba Saboda Yana Addinin Musulunci, Kakakin Majalisa

  • Abok Ayuba Nuhu, kakakin majalisar dokokin jihar Plateau ya ce ba zai kashe mahaifinsa don yana addinin musulunci
  • Abok ya yi wannan jawabin ne wurin wani taron zaman lafiya da dan majalisa mai wakiltar Jos ta Arewa, Ibrahim Baba Hassan ya shirya
  • A cewar Abok, duk masu tada rikici da sunan addini makaryata ne domin babu addinin da ya koyar da rikici kuma zaman lafiya ya fi komai

Jos, Plateau - Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Plateau, Honarabul Abok Ayuba Nuhu ya ce ba zai kashe mahaifinsa ba saboda addininsu daban, rahoton Daily Trust.

Rikicin Jos: Ba Zan Kashe Mahaifina Ba Saboda Yana Addinin Musulunci, Kakakin Majalisa
Taswirar Jihar Plateau. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Abok ya yi wannan furucin ne yayin taron zaman lafiya da aka shirya mai taken Zaman Tare: Magani domin zaman lafiya da cigaba wadda dan majalisa mai wakiltar Jos ta Arewa maso Arewa Hon Ibrahim Baba Hassan ya shirya.

Kara karanta wannan

Ana Amfani da Jiragen Alfarma Wajen Satar Albarkatun Zinari a Najeriya, Minista Ya Fallasa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gudanar da taron ne a dakin taro na Lamonde da ke Jos, babban birnin jihar Plateau.

Kakakin majalisar wanda mahaifinsa musulmi ne ya ce wadanda ke cewa suna fada a jihar saboda addini makaryata ne, yana mai cewa suna fakewa da sunan addini ne domin cimma wata bukata ta kansu domin babu addinin da ya koyar da rikici.

Ya kuma yi kira da al'ummar jihar da su cigaba da zama lafiya da juna ba tare da la'akari da babancin addini ba domin babu abin da ya fi zaman lafiya muhimmanci.

Sultan: Allah bai yi kuskure ba da ya haɗa mu zama tare a matsayin ƴan Nigeria

A wani labarin daba, mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar na III, ya bukaci dukkan kabilun Nigeria su cigaba da zama a matsayin yan uwan juna domin Allah bai yi kuskure ba da ya hada mu zama a matsayin kasa daya, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Dan mai gida ya yi wa ɗan hanya duka har sai da ya ce ga garinku

Da ya ke jawabi a matsayinsa na shugaba a wurin taron bada lambar yabo na shugabanci na 2020 a ranr Alhamis a Abuja, Sultan ya ce raba kasar ba zai magance matsalolin da kowace kabilar ke fama da shi ba amma hada kai tare a warware matsalar ce ta fi amfani.

Sultan ya ce wadanda ke amfani da addini domin raba kan mutane ba za su yi nasara ba domin mutanen kasar ba za su biye musu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags:
Jos