Najeriya na Tangal Tangal, Tinubu Zai Runtumo Sabon Bashin Naira Tiriliyan 4.2

Najeriya na Tangal Tangal, Tinubu Zai Runtumo Sabon Bashin Naira Tiriliyan 4.2

  • Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da shirin karbo rance na Naira tiriliyan 4.199 domin tallafa wa tattalin arzikin Najeriya
  • Ministan tattali, Wale Edun, ya bayyana cewa za a yi amfani da kudin wajen inganta tattalin arzikin ta hanyar manyan ayyuka
  • Majalisar ta kuma amince da shirin saka hannun jari a gidaje wanda zai taimaka wajen rage gibin gidaje da samar da ayyukan yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da shirin shugaba Bola Tinubu na karbo sabon bashin Naira tiriliyan 4.199 (dala biliyan $2.2).

An ce bashin na dala biliyan 2.2 ya haɗa da dala biliyan 1.7 da kuma dala miliyan 500 na shirin SUKUK da za a karbo.

Gwamnatin tarayya ta fara shirin karbo sabon bashi na dala biliyan 2.2
Majalisar zartarwa ta amince Tinubu ya runtumo sabon bashin $2.2bn. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Bola Tinubu zai sake karbo bashin $2.2bn

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu na shirin gabatar da Naira tiriliyan 48 a matsayin kasafin kudin 2025

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa manufar wannan rancen shi ne ingantawa tare da kuma tallafa wa sake fasalin tattalin arzikin kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan Kudi, Wale Edun, ya bayyana hakan bayan taron FEC wanda shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a fadar gwamnatin tarayya ranar Alhamis.

Edun ya bayyana cewa, idan majalisar dokoki ta amince da kudurin, Najeriya za ta iya samun kuɗi daga kasuwar duniya ta hanyar karbo rance na Euro da SUKUK.

Ya bayyana wannan rance a matsayin “wani bangare na yarjejeniyar Euro da kuma yarjejeniyar shirin SUKUK” wadanda za su kammala shirin rance na ƙasa.

Tasirin manufofin Tinubu a kasuwar duniya

A cewarsa, damar da Najeriya ta samu a kasuwar duniya alama ce ta amincewa da shirin Tinubu na farfaɗo da tattalin arziki, a cewar rahoton Punch.

Edun ya ce:

"Samun damar shiga kasuwar duniya yana nuna goyon baya ga shirin tattalin arzikin shugaban kasa, musamman kan farashin fetur da sauyin canjin kudi."

Kara karanta wannan

Wata 1 da birne matarsa, wani fitaccen dan wasan kwallon kafar Najeriya ya rasu

Majalisar ta kuma amince da shirin saka hannun jarin Naira biliyan 250 a gidaje, wanda zai taimaka wajen samar da ayyuka da rage gibin gidajen Najeriya.

Tinubu zai ranto $2.25bn daga Bankin Duniya

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kuduri aniyar karbo sabon bashin dala biliyan 2.25 daga Bankin Duniya.

Ministan kuɗi, Wale Edun wanda ya tabbatar da hakan inda ya ce za ayi amfani da kudin wajen farfado da tattalin arzikin kasar da ke tangal tangal.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.