Shugaba Tinubu Na Shirin Gabatar da Naira Tiriliyan 48 a Matsayin Kasafin Kudin 2025
- Gwamnatin tarayya za ta gabatar da kasafin kudin 2025 da ya kai Naira tiriliyan 47.9, domin inganta tattalin arziki
- Majalisar zartarwa ta tarayya ce ta amince da kasafin kudin a taronta na yau wanda shugaba Bola Tinubu ya jagoranta
- Kasafin kudin ya tanadi sayar da gangar danyen mai a kan $75 tare da burin samar da ganga miliyan 2.06 kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin Najeriya za ta gabatar da kasafin kudi na 2025 da ya kai Naira tiriliyan 47.9, domin inganta ayyuka da tattalin arzikin kasa.
Ministan tsare-tsaren kasafin kudi da tattalin arziki, Atiku Bagudu, ya bayyana haka bayan taron majalisar zartarwa da Bola Tinubu ya jagoranta.

Source: Twitter
An fara maganar kasafin kudin 2025
Majalisar ta amince da tsarin samar da kudin da za a kashe daga 2025 zuwa 2027 da kuma yadda za a kashe su a shekaru ukun, inji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kasafin ya tsayar da farashin gangar danyen mai a kan $75, wanda zai bada tabbacin daidaituwar kudaden shiga da duk da hawa da saukar farashin man a duniya.
Ana sa ran Najeriya za ta samar da ganga miliyan 2.06 na danyen mai a kowace rana, don kara kudaden shiga na gwamnati daga sayar da man.
Abubuwan da kasafin 2025 zai shafa
Majalisar ta kuma sanya farashin musayar dala da Naira a kan N1,400, domin rage tsadar kayayyaki da tabbatar da darajar Naira a kasuwanni.
Ana sa ran kasafin zai jawo bunkasar tattalin arziki da kashi 6.4%, wanda ake sa ran zai rage rashin ayyukan yi da talauci a kasar baki daya.
Kasafin kudin zai bai wa gwamnati damar zuba jari a ababen more rayuwa da tsaro, tare da shawo kan matsaloli bayan majalisa ta amince da shi.
Kasafin 2024 da shugaba Tinubu ya gabatar
A wani labarin, mun ruwaito cewa kasafin shekarar 2024 da shugaba Bola Tinubu ya shirya gabatarwa ya kai Naira tiriliyan 26.
Ministan kasafi da tsare-tsaren ƙasa, Atiku Bagudu, ne ya bayyana adadin kuɗin da kasafin 2024 ya ƙunsa bayan karƙare taron majalisar zartarwa (FEC).
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

