"Yan Ta'adda Suna Kashe Mutane Son Ransu:" An Shawarci Arewa Ta Farka

"Yan Ta'adda Suna Kashe Mutane Son Ransu:" An Shawarci Arewa Ta Farka

  • Hukumar kare hakkin dan Adam ta koka bisa yawaitar kashe mutane da yan ta'adda ke yi a kasar nan tun daga Janairu
  • A wani taron hadin gwiwa da tarayyar Turai da hukumar ta yi a Najeriya, ta bayyana adadin mutanen da aka kashe
  • A zantawarsa da Legit, shugaban gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, Haruna Ayagi ya ce abin ya kazanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa (NHRC), ta ce akalla mutum 1,463 yan ta'adda su ka kashe daga Janairun 2024 har zuwa watan Satumba.

Hukumar ta fadi haka ne a taron ƙara wa juna sani da hukumar ta gudanar tare da hadin gwiwar kungiyar Tarayyar Turai.

Kara karanta wannan

Lakurawa sun ji ruwan alburusai, sun fara guduwa daga Najeriya

Arewa
Yan ta'adda sun kashe mutane da dama a Arewa Hoto: Stringer
Asali: Getty Images

TRT ta wallafa cewa wani babban jami’i a hukumar Hilary Ogbonna ya bayyana cewa haka kuma an sace mutum 1,172 a watanni 11 na shekarar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yan ta'adda na kisa:" Kungiyar kare hakki

Shugaban gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, Kwamred A Haruna Ayagi ya bayyana cewa mutanen da aka kashe sun haura adadin NHRC.

Ya shaidawa Legit cewa adadin da NHRC ta fada iya alkaluman da ta iya tattarawa ne kawai, amma Arewa ta na cikin mawuyacin hali.

Jihohin Arewa da ta'addanci ya fi kamari

Kwamred Ayagi ya ce jihohin Zamfara, Kebbi, Sakkwato da Neja sun yi kaurin suna wajen matsalolin ta'addanci.

Ya bayyana cewa a kullum, sai an kashe wasu daga cikin mazauna jihohin, duk da gwamnoni 19 da yan majalisu da shiyyar Arewa ke da su.

An Arewa shawara a kan ta'addanci

Kwamred A Haruna Ayagi ya yi mamakin yadda gwamnonin yankin 19 da sauran shugabanni su ka gaza sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Kara karanta wannan

Laifin Lakurawa ya shafi Fulani, an kashe mutane 6 a Kebbi

Kwamred Ayagi ya na ai fatan shugabanni za su farka domin magance matsalolin da su ka addabi jama’arsu kafin matsalar ta fi haka girma.

Sojoji sun sako yan ta'adda a gaba

A baya mun ruwaito cewa rundunar sojojin kasa da na saman kasar nan sun hadu wajen kai samame sansanin wasu daga cikin mayakan Lakurawa da su ka bulla a jihohin Arewa.

Sabuwar kungiyar Lakurawa ta fara daukar hankalin manyan Arewa da sauran masu ruwa da tsaki biyo bayan ganin irin mummunar akidarsu mai kama da ta Boko Haram da ISWAP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.