Ondo 2024: Aiyedatiwa da Wasu Jerin Ƴan Takarar Gwamna 3 da Za Su Iya Lashe Zabe
- Zaɓen Ondo 2024 na dauke da manyan 'yan takara hudu: Lucky Aiyedatiwa, Ajayi Agboola, Otunba Akingboye da Sola Ebiseni
- Kowane dan takara na da burin inganta jihar Ondo, ta fuskar habaka tattalin arziki, ababen more rayuwa, lafiya, da rage cin hanci
- Yayin da zaɓen ke gabatowa, Legit Hausa ta yi bayanin manyan 'yan takarar hudu da daya daga cikinsu ake sa ran zai yi nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo - A yayin da zaben gwamnan Ondo ke kara gabatowa, manyan ‘yan takara sun daukarwa al'ummar jihar alkawura mabanbanta, da tunanin samun kuri'u a ranar zabe.
Ana hasashen cewa, 'yan takara hudu ne za su fi daukar hankali a zaben, inda daya daga cikinsu zai iya zama gwamnan jihar Ondo na gaba.
Ga jerin bayanan kowane ɗan takara da manufofin da ya gabatarwa al'ummar jihar yayin da al'umma ke shirin kada kuri'a a ranar Asabar mai zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ondo: 'Yan takarar da za su iya lashe zabeL
1. LuckyAiyedatiwa (APC)
Gwamna Lucky Aiyedatiwa, dan takarar APC sananne ne a fagen siyasar Ondo, wanda ke da gogewa a aikin gwamnati.
Manufar yakin neman zabensa ta mayar da hankali ne kan karfafa ababen more rayuwa da kiwon lafiya a fadin jihar domin inganta rayuwar jama'a.
Bayan mutuwar Oluwarotimi Akeredolu ne aka rantsar da Lucky Aiyedatiwa a matsayin gwamnan jihar Ondo, a watan Disambar 2023, a cewar rahoton BBC.
A yakin neman zaben gwamnan jihar na 2024, Aiyedatiwa ya yi alkawarin karfafawa matasa ta hanyar ba su horon sana'o'i, samar da ayyukan yi, da rage talauci.
2. Ajayi Agboola (PDP)
Ajayi Agboola, dan takarar PDP, yana da masaniya game da matsalolin da ke fuskantar Ondo, kasancewar ya rike mukaman gwamnati daban daban.
Agboola ya ce zai farfado da tattalin arziki, magance rashin aikin yi na matasa ta hanyar tallafawa kasuwanci da ba da horo na sana'o'i, a cewar rahoton Premium Times.
A yakin neman zabensa, Agboola ya ce zai fadada ayyukan kiwon lafiya da shirye-shiryen jin dadin jama'a domin tallafawa gajiyayyu a cikin al'ummar jihar.
Ya ce jihar Ondo za ta bunkasa ta hanyar bunkasa tattalin arziki da zuba jari mai yawa a ilimi, yana mai yakinin gina jajirtacciyar al'umma mai dogaro da kai.
3. Otunba Bamidele Akingboye (SDP)
Otunba Bamidele Akingboye daga jam'iyyar SDP ya yi alkawarin bunkasa kasuwanci, kawo sauye-sauyen tattalin arziki da za su magance kalubalen da Ondo ke fuskanta.
Jaridar Vanguard ta rahoto Akingboye, a yakin neman zabensa, ya ce gwamnatinsa za ta zamo ta kowa, kuma zai bunkasa kauyuka ta yadda za su amfana da arzikin jihar.
Akingboye ya kuma jaddada manufofinsa na kawo tsare-tsaren muhalli masu dorewa, inda ya dauki alkawarin mayar da Ondo jihar da ke kula da muhalli.
Dan takarar na SDP ya ce zai inganta yawon shakatawa da masana'antu na kere-kere domin habaka aikin yi na cikin gida da kuma bunkasa tattalin arziki.
4. Sola Ebiseni (LP)
Sola Ebiseni na jam'iyyar LP ya daukarwa al'ummar Ondo alkawarin yin shugabanci na gaskiya mai cike da adalci idan aka bashi dama, a cewar rahoton The Guardian.
Manufarsa ta fi mayar da hankali kan yaki da cin hanci a cikin hukumomi domin tabbatar da kyakkyawan sarrafa albarkatun jihar.
Ebiseni ya kuma jaddada burin kawo sauyi a aikin gona, yana mai goyon bayan sababbin dabarun noma don karfafa tsaro na abinci da dorewar tattalin arziki.
Haka nan yana son magance gibin ayyukan yi a jihar, musamman a fannonin lafiya da ilimi, ta hanyar tabbatar da rabon albarkatu da samar da wasu ayyukan.
Kotu ta kori dan takarar gwamnan Edo
A wani labarin, mun ruwaito cewa kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta soke takarar Olusola Ebiseni na jam'iyyar LP a zaɓen gwamnan jihar Ondo.
Kotun ta bayyana cewa ta amince da ƙorafin da jam'iyyar LP ta gabatar kan Olusola Ebiseni da wasu mutum biyu dangane da zaben fitar da gwanin jam'iyyar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng