Shugaban NAHCON Ya Je Majalisa, Ya Tabbatar da Zargin da Ake Tsoro a Aikin Hajji
- Kwamitin majalisar wakilai ya zargi hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) da tafka badakaloli iri iri a harkar gudanar da aikin hajji
- Shugaban kwamitin da aka kafa ya binciki hukumar, Sada Soli ya yi zargin a lokacin da shugaban hukumar ya bayyana a gabansu
- Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya tabbatar da zargin majalisa na cewa ana tafka badakala a hukumarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Shugaban hukumar aikin hajji ta kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan ya tabbatar da cewa ana samun badakalar a hukumar.
Ya tabbatar da haka ne a lokacin da ya bayyana a gaban majalisar wakilai tare da tsokaci kan maganar shugaban kwamitin binciken ayyukan hukumar, Hon. Sada Soli.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin shugaban NAHCON a ranar 10 Oktoba, 2024
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa na zargin badakala a hukumar hajji
Jaridar The Guardian ta wallafa cewa dan majalisar wakilai daga Katsina, Sada Soji ya yi zargin tafka badakala a hukumar aikin hajjin Najeriya.
A martaninsa bisa zargin, sabon shugaban hukumar ta kasa, Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan ta tabbatar da zargin da majalisar ta yi.
Majalisa na binciken hukumar kula da hajji
Majalisar wakilan kasar nan ta samar da kwamiti da zai binciki badakalar N90bn da ake zargin an aikata a hukumar aikin hajji da kasa da hukumar jin dadin alhazai ta FCTA.
Ana zargin hukumar da rufa-rufa ta fuskar bayar da tallafin Dala a aikin hajjin 2024 da wasu badakaloli a baya.
Ana kuma zargin NAHCON da ba alhazan $400 kacal duk da sun biya Naira miliyan takwas ga mahukuntan Najeriya.
Zargin badakala a hukumar hajji
A baya mun ruwaito cewa daya daga cikin gwamnonin kasar nan ya bukaci hukumomi su binciki hukumar aikin hajji ta kasa (NAHCON) bisa zargin badakala.
Gwamnan jihar Neja, Muhammadu Umaru Bago, ta cikin sanarwar da babban sakataren yada labaransa ya fitar, ya ce ana rage kudin guzurin alhazai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng