An Rasa Rayuka bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Sojoji a Wani Shingen Bincike

An Rasa Rayuka bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Sojoji a Wani Shingen Bincike

  • Wasu ƴan bindiga sun kai farmaki kan shingen bincike na dakarun sojoji a ƙaramar hukumar Umuahia ta Kudu a jihar Abia
  • Ƴan bindigan ƙungiyar IPOB/ESN sun farmaki jami'an tsaron ne da sanyin safiyar ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamban 2024
  • Jami'an sojoji biyu sun rasa rayukansu a ƙoƙarin da suka yi na daƙile harin ƴan bindigan masu ɗauke da makamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Ƴan bindiga sun kai farmaki a sansanin sojoji da safiyar ranar Laraba inda suka hallaka jami'an tsaro mutum biyu a jihar Abia.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Ekenobizi a yankin Umuopara wanda ke kan iyaka da jihohin Imo da Abia.

Yan bindiga sun farmaki sojoji a Abia
'Yan bindiga sun hallaka sojoji a Abia Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wata majiya daga ɓangaren sojoji da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa harin ya auku ne da misalin ƙarfe 6:18 na safe, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Ana batun Lakurawa a Arewa, sojoji sun yi wa 'yan bindiga raga raga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka farmaki sojoji

Ƴan bindigan sun je shingen binciken ne a wata farar mota ƙirar Lexus (350/400), duk da cewa ba a tantance adadinsu ba.

Laftanar Kanal Jonah Unuakhalu na rundunar haɗin gwiwa ta Operation Udoka ya tabbatar da aukuwar harin a ranar Laraba.

"Da safiyar yau, 13 ga watan Nuwamban 2024, ƴan ta'addan IPOB/ESN sun kai wa jami'an tsaro na rundunar haɗin gwiwa ta Operation Udoka hari a shingen bincike da ke kan titin hanyar Umuahia-Owerri a ƙaramar hukumar Umuahia ta Kudu."
"A yayin farmakin, dakarun sojojin sun samu nasarar daƙile harin inda suka tilastawa maharan arcewa ɗauke da raunuka tare da barin motoci ƙirar Sienna da Lexus waɗanda suka yi amfani da su wajen kai harin."
"Sai dai, a artabun da aka yi, jami'an sojoji biyu sun rasa rayukansu."

- Laftanar Kanal Jonah Unuakhalu

Sojoji sun fatattaki ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na rundunar Operation FANSAN YANMA sun samu nasara kan ƴan bindiga a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram sun zo da ta'addanci, sun yi barna a Borno

Dakarun sojojin sun yi nasarar daƙile harin da ƴan bindiga suka kai a Gatawa cikin ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto ranar Talata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng