An Yi Rashi: Tsohon Alƙalin Kotun Koli Ya Kwanta Dama, Tinubu Ya Tura Sako
- Shugaba Bola Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon alƙalin Kotun Koli a Najeriya, Mai shari'a Emmanuel Obioma Ogwuegbu
- Tinubu ya bayyana rashin Ogwuegbu a matsayin babban rashi ga iyalansa da bangaren shari'a da Najeriya baki daya
- Marigayin wanda dan asalin jihar Imo ne ya rasu a jiya Talata 12 ga watan Nuwambar 2024 bayan fama da jinya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon alƙalin Kotun Koli a Najeriya ya yi bankwana da duniya yana da shekaru 91.
Marigayin mai suna Emmanuel Obioma Ogwuegbu ya rasu ne bayan fama da jinya mai tsayi.
Tinubu ya jajanta mutuwar tsohon alƙalin kotu
Hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya tura sakon ta'azziya ga iyalan marigayin inda ya ce an tafka babban rashin jajirtacce.
An haifi marigayi Ogwuegbu a Amainyi da ke karamar hukumar Ihitte-Uboma a jihar Imo a 1933.
Shugaban Najeriyan ya bayyana irin gudunmawa da Obioma Ogwuegbu ya bayar wurin inganta ɓangaren shari'a.
"An yi asarar jajirtaccen alkali" - Tinubu
Tinubu ce mutuwar Ogwuegbu ta bar babban gibi wanda zai dauki lokaci kafin maye gurbinsa cikin sauki.
"Shugaba Bola Tinubu ya tura sakon ta'azziya ga iyalan marigayi tsohon alƙalin Kotun Koli, Emmanuel Obioma Ogwuegbu kan rasuwarsa."
"Tinubu ya kuma jajantawa bangaren shari'a gaba daya inda ya ce an yi rashin jajirtacce."
"Ya bayyana irin gudunmawar da marigayin ya bayar a bangaren shari'a wurin yin hukunci ba tare da wariya ko tsoro ba."
- Bola Tinubu
Tsohon shugaban PDP a Abuja ya rasu
A baya, kun ji cewa Allah ya yi wa tsohon shugaban jam'iyyar PDP reshen Abuja, Alhassan Gwagwa rasuwa ranar Litinin, 11 ga watan Nuwamba, 2024.
An ruwaito cewa jigon PDP ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya a gidansa da ke Gwagwa, ƙaramar hukumar birni AMAC a Abuja.
Manyan jam'an gwamnati da ƴan siyasa daga Nasarawa, Neja da Abuja sun halarci sallar jana'izar marigayin a jiya Litinin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng