Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa tsohon Alƙalin kotun kolin Najeriya rasuwa
- Allah yayi wa tsohon alkalin kotun koli, Mai shari'a Abubakar Bashir Wali rasuwa a garin Kano
- Wali yana daga cikin masu shari'a na farko a Arewacin Najeriya kuma alkalin farko na kotun daukaka karar shari'ar musulunci da ya fara daukaka zuwa alkalin kotun koli
- Kamar yadda majiya daga iyalan mamacin ta sanar, tsohon mai shari'ar ya rasu ne bayan gajeriyar jinya a Kano kuma za a yi jana'izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar
Allah yayi wa tsohon alkalin kotun koli, Abubakar Bashir Wali rasuwa a yau Talata, 21 ga watan Janairu 2019. Mai shari'ar ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiyar da yayi a garin Kano, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Wali yana daga cikin masu shari'a na farko a Arewacin Najeriya kuma alkalin farko na kotun daukaka kara na shari'ar musulunci da ya fara daukaka zuwa matsayin alkalin kotun koli na Najeriya.
Tsohon mai shari'ar na daya daga cikin kwararru a fannin shari'a a Arewacin Najeriya.
Ya fara aiki ne a matsayin alkalin kotun majistare.
DUBA WANNAN: Yadda matar aure da umurci mijinta ya rika kwanciya da mahaifyarta saboda neman abin duniya
Kamar yadda majiya daga iyalansa ta bayyana, a matsayinsa na Musulmi, za a yi jana'izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar da rana a garin Kano.
Har yanzu dai iyalan mamacin basu sanar da ciwon da yayi ajalin tsohon mai shari'ar ba.
Tsohon alkalin kotun kolin ya rasu ne a ranar da ake sauraron hukuncin karshe kan shari'un jihohin Binuwai da Adamawa a kotun kolin a kan zaben gwamnoni wanda aka yi a ranar 9 ga watan Maris na 2019.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng