Gwamna Ya Ayyana Ilimin Firamare da Sakandire Kyauta a Jiharsa, An Gargadi Iyaye

Gwamna Ya Ayyana Ilimin Firamare da Sakandire Kyauta a Jiharsa, An Gargadi Iyaye

  • Gwamnatin jihar Abia ta sanar da ayyana ilimin firamare da sakandare kyauta daga Janairun 2025 domin saukakawa iyaye
  • Shirin ba da ilimi kyauta na kunshe ne a cikin dokar 'Haƙƙin Yara ta Jihar Abia' ta 2006 domin inganta ilimi ga kowane ɗalibi
  • Kwamishinan sadarwa da al'adu, Okey Kanu, ya ce matakin zai taimaka wajen kawar da matsalar ke hana yara samun ilimi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abia - Gwamnatin Abia ta ayyana ilimin firamare da na sakandare kyauta daga Janairu 2025 da nufin rage jahilci a tsakanin yaran jihar.

An ce shirin ba da ilimi kyautan ya dace da dokar 'Haƙƙin Yara ta Jihar Abia ta 2006', wanda ke tabbatar da niyyar gwamnati na samar da ingantaccen ilimi ga kowane ɗalibi.

Gwamantin Abia ta yi magana bayan ayyana ilimin firamare da na sakandare kyauta
Gwamnati ta ayyana ilimi kyauta a Abia Hoto: SOPA Images / Contributor
Asali: Getty Images

Gwmanatin Abia ta ayyana ilimi kyauta

Kara karanta wannan

Mawaki Rarara ya biya kudin sadakin Aishatul Umairah? Jarumar ta fadi gaskiya

Okey Kanu, kwamishinan sadarwa da al'adu, ya ce shirin zai kawar da matsalar kudade da ke hana yara samun ilimi a jihar Abia, a cewar rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kanu ya kara da cewa, daga Janairu 2025, iyaye ko masu kula da yara da suka ki tura yaransu makaranta za su fuskanci hukunci kamar yadda dokar ta tanadar.

Ya jaddada cewa rashin bin wannan umarni na ba da ilimi kyauta zai jefa iyaye a matsala, kuma za a hukunta wadanda suka sabawa dokar ba tare da dagin kafa ba.

Gwamnatin Abia ta gargadi iyayen yara

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati ba za ta karfi wani uzuri daga iyayen da suka ki tura yaransu makaranta ba daga Janairu 2025, kuma dokar za ta yi aiki a kansu.

Punch ta rahoto Mista Kanu ya bayyana cewa rashin kuɗi ba zai zama dalilin rashin samun ilimi a jihar Abia ba daga Janairu 2025, dukan yaran jihar za su ci gajiyar ilimi kyauta.

Kara karanta wannan

'Ka hana Wike, gwamnoni ba alkalai motoci da gidaje,' SERAP ta fadawa Tinubu

Baya ga manufar ilimi kyauta, Kanu ya jaddada cewa ana gudanar da gyaran ilimi a jihar, ciki har da inganta gine-gine, da ba ma'aikatan ilimi gagarumar goyon baya.

An ayyana ilimi kyauta a Taraba

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya ayyana karatun makarantar Firamare da Sakandare kyauta a jihar.

Gwamna Kefas ya yi wannan albishir na ayyana ilimi kyauta ga dukkanin daliban jihar yayin da ya kai ziyara makarantar Firamare da ke Wukari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.