Mun kashe 3.4bn a bangaren tilastawa da bada ilimi kyauta a Kano - Ganduje

Mun kashe 3.4bn a bangaren tilastawa da bada ilimi kyauta a Kano - Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta kashe naira biliyan 3.4 wajen aiwatar da shirin wajabtawa da kuma bayar da ilimi kyauta a jihar, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana.

Ya bayyana hakan a Kano a lokacin gabatar da takardar kudi na naira miliyan 20 ga kananan hukumomi 44 na jihar a ranar Asabar, wanda jimillarsa ya kama naira miliyan 880, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce an yi rabon kudin ne domin kari ga shirin gyaran makarantun firamare da sakandare a fadin jihar.

Ganduje ya ce: “Kano ta ware sama da kaso 26 cikin 100 na kasafin kudinta na shekara ga sashin ilimi wanda ya yi daidai da amincewar UNESCO.

“Mun yi nasarar samar da wannan kudi ta hanyar sakin 5% na kudaden shigarmu, 5% na kudaden kananan hukumomi, 2% na duk wani kwangila da aka bayar a jiharmu tare da gudunmawa daga UBEC, da sauran abokan harka na ci gaban kasa da kasa ta fannin ilimi.”

Gwamnan ya kara da cewar jihar ta samu wannan nasara ne saboda tana da kudirin siyasa sannan kuma manyan cibiyoyi sun samar da isassun kudade.

Mun kashe 3.4bn a bangaren tilastawa da bada ilimi kyauta a Kano - Ganduje
Mun kashe 3.4bn a bangaren tilastawa da bada ilimi kyauta a Kano - Ganduje Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Har ila yau da yake jawabi, babban sakataren hukumar makarantun firamare a jihar (SUBEB), Alhaji Danlami Hayyo ya ce jihar ta yi amfani da naira biliyan 3.4 wajen gina ajujuwa sama da 407 da kuma gyara wasu fiye da 700 da suka tsufa.

KU KARANTA KUMA: Zamfara za ta fara yankewa masu tukin ganganci hukuncin kisa bayan mutuwar wasu magoya bayan gwamnan su 15

An kuma gina bandaki fiye da 460, an samar da kujeru 40,000, da kuma gina tuka-tuka na ruwa guda 200 a makarantun da ke fadin jihar.

“Kafin zuwan shirin ilimi kyauta da wajabta shi a Kano, muna da dalibai miliyan 1.5 ne kacal a makarantunmu, amma a yau bayan samar da manufar, akwai yara sama da miliyan 3.8 a makarantu,” in ji shi.

Hakazalika, kwamishinan ilimi na jihar, Sanusi Sa’id Kiru ya ce jihar ta rigada ta gina makarantun kwana na Almajirai guda uku a mazabu sannan tana shirin gina wasu 130 na makarantun mata a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel