Bayan Barazanar NLC, Gwamna a Arewa Ya Amince da Sabon Mafi Karancin Albashi
- Gwamnan jihar Taraba ya bi sahun sauran gwamnoni a Najeriya wajen amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatansu
- Dakta Agbu Kefas ya amince zai fara biyan ma'aikatan gwamnati a jihar Taraba sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 duk wata
- Shugaban ma'aikatan jihar ya ce amincewa da sabon albashin ya yi daidai da ƙudirin gwamnati na inganta rayuwar masu yi mata aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Taraba - Mai girma Gwamnan Taraba Agbu Kefas ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan jihar.
Gwamna Agbu Kefas ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan gwamnati a jihar Taraba.
Gwamnan Taraba ya amince da albashin N70,000
Tashar talabijin ta Channels tv ta rahoto cewa shugaban ma’aikatan jihar, Paul Maigida ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ma'aikatan ya bayyana cewa za a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ne daga watan Nuwamban 2024.
"Ina so na sanar da ku cewa mai girma gwamnan jihar Taraba, Dr Agbu Kefas, ya amince da aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma'aikata a jihar Taraba daga watan Nuwamba, 2024."
- Paul Maigida
Kungiyar NLC ta taso gwamnoni a gaba
Maigida Ya bayyana cewa fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ya yi daidai da ƙudirin gwamnati mai ci na inganta rayuwar ma'aikata a jihar.
Amincewa da sabon mafi ƙarancin albashin na zuwa ne bayan ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta umarci ma'aikata su fara yajin aiki.
Babu mamaki daga ranar 1 ga watan Disamba a shiga yajin aiki a jihohin da ba a fara biyan sabon albashin ba.
Gwamna Kefas ya yi abin a yaba
Hassan Kundi mazaunin jihar Taraba ya shaidawa Legit Hausa cewa amincewa da sabon mafi ƙarancin albashin abin a yaba ne.
"Eh lallai wannan abin a yaba ne duba da yadda rayuwa ta yi tsada ma'aikata za su samu sauƙin wasu abubuwan."
- Hassan Kundi
Karanta wasu labaran kan mafi ƙarancin albashi
- Mafi karancin albashi: NLC ta sanar da lokacin fara yajin aiki
- Mafi karancin albashi: Jerin Jihohin da ba Su Fara Biyan Ma'aikata N70,000
- Gwamna Uba Sani ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan Kaduna
Gwamna ya amince da albashin N80,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin Oyo ƙarƙashin jagorancin Seyi Makinde ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar.
Gwamna Seyi Makinde ya amince da sabon mafi ƙarancin albashin N80,000 wanda za a riƙa biyan ma’aikatan jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng