Wata 1 da Birne Matarsa, Wani Fitaccen Dan Wasan Kwallon Kafar Najeriya Ya Rasu
- Fitaccen dan wasan kwallon Najeriya, Gift Atulewa ya rasu yana da shekaru 38 sakamakon abin da ake zargi da ciwon zuciya
- An ce watan da ya gabata ne aka birne matarsa da ta rasu, wanda ake zargin hakan ya kara jawo tabarbarewar rashin lafiyarsa
- Hukumar kwallon kafar Delta ta bayyana cewa mutuwar Atulewa babban rashi ne ga duniyar kwallon kafa da Najeriya baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Delta - Duniyar kwallon kafar Najeriya na jimamin rasuwar dan wasan kwallon kafa na kasa, Gift Atulewa, wanda ya rasu yana da shekaru 38.
Azuka Chiemeka, mai magana da yawun hukumar kwallon kafa ta jihar Delta, ya tabbatar da rasuwar Gift Atulewa da safiyar ranar Talata.
Atulewa: 'Dan wasan kwallon Najeriya ya rasu
Mr. Azuka ya shaida wa jaridar Premium Times cewa dan wasan ya rasu sakamakon matsalar hawan jini da misalin karfe 7:00 na safe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“A watan da ya gabata ne muka yi bikin birne matarsa da ta rasu; hakan na iya zama silar tabarbarewar lafiyarsa. Yana fama da matsalar hawan jini."
- Mista Azuka.
Mista Azuka ya bayyana cewa:
“Kwanaki biyu da suka wuce, jikin nasa ya yi tsanani. An kai shi asibiti inda aka yi masa gwajin zazzabin cizon sauro, amma aka ga hawan jininsa na kara tashi."
Abin sani game da dan wasan kwallon
Yayin da yake bayyana ayyukan da Atulewa ya yi kwanan nan, Mr. Azuka ya kara da cewa, “yana taka leda a gasar tsofaffin ‘yan wasan kasa da ake gudanarwa a jihar Delta."
An ce dan wasan ya zura kwallo ta farko a gasar sama da mako uku da suka gabata ta hanyar bugun tazara da aka san shi da kwarewa a kai.
Har ila yau, kwanan nan ya dawo daga Côte d’Ivoire inda ya kammala horo na zama mai koyar da kwallon kafa, duk da cewa ba zai samu damar amfani da wannan takardar shaidar ba.
Atulewa na daga cikin tawagar Najeriya (U-20) da suka halarci gasar cin kofin kwallon kafa ta matasa ta duniya a shekarar 2005 da aka gudanar a kasar Netherlands.
Dan kwallon Najeriya ya mutu a filin wasa
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon dan kwallon kungiyar Jigawa United, Hadi Bala Ado, ya yanke jiki ya fadi matacce yana tsaka da buga wasa.
Hukumar kwallon kafar The Castilla-La Mancha ta ce matashin dan kwallon na Najeriya ya yanke jiki ya fadi ba tare da wata matsalar zahiri ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng