'Zaluncin Ya Yi Yawa,' Ƴan Bindiga Sun Cinnawa Gonakin Mutane Wuta a Jihar Arewa

'Zaluncin Ya Yi Yawa,' Ƴan Bindiga Sun Cinnawa Gonakin Mutane Wuta a Jihar Arewa

  • 'Yan bindiga sun kai hari a gonakin Kwaga da Unguwar Zako a Birnin Gwari, jihar Kaduna, inda suka kone gonaki da dama
  • An rahoto cewa manoman da abin ya shafa sun nuna matukar damuwarsu kan asarar da suka tafka a wannan harin 'yan bindigar
  • Shugaban kungiyar hada kan mutanen Birnin Gwari da Neja, ya yi ikirarin cewa 'yan bindigar na karkashin Yellow Jamboros

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Miyagun 'yan bindiga sun kona gonakin mutane a Kwaga da Unguwar Zako da ke cikin karamar hukumar Birnin Gwari, jihar Kaduna.

An ce 'yan bindigar sun kona bukkuokin masara da aka girbe a gonaki shida, inda masu gonakin suka shiga cikin matsananciyar damuwa.

'Yan bindiga sun kona gonakin mutane a garuruwan Kaduna
Manoma Kaduna sun tafka asara bayan 'yan bindiga sun kona gonakinsu.
Asali: Original

Kaduna: 'Yan bindiga sun kona gonaki

Wani bidiyo da jaridar Daily Trust ta samu ya nuna amfanin gonar da ya yi saura a cikin gonakin da aka kona, inda manoma ke taya juna jaje.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi ta'asa, sun bindige dan sanda, sun sace yan kasashen waje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Lahadi lokacin da 'yan bindigar suka shiga gonakin suna kona bukkokin masaran.

Daya daga cikin manoman da abin ya shafa, Kabiru Halilu Kwaga, wanda ya girbe buhunan masara sama da 160 a bara ya koka da barnar da aka yi masu.

Kabiru Halilu Kwaga ya ce ya sanya a ranshi cewa zai samu karin amfanin gona a wannan shekarar, amma 'yan bindigar sun kona amfanin gonarsa.

Manoma sun yi takaicin rasa gonakinsu

Wani manomi, Surajo Kwaga, wanda ya girbe buhuna 40 na masara a bara, ya rasa dukkanin amfanin gonarsa a bana.

Haka kuma Malam Dan Gido, wanda ya girbe buhuna 50 a bara, kuma yake sa ran samun buhuna 65 wannan shekarar, shi ma ya rasa komai.

Jibril Haladu Kwaga, wani manomi, shi ma ya rasa masararsa a wannan hari. Manoman da abin ya shafa suna addu'ar samun sakayya.

Kara karanta wannan

'An yi artabu': Ƴan banga, mafarauta sun halaka ƴan bindiga, an ceto mutane 14

'Ƴan dabar Yellow Jamboros ne' - Ishaq

Ishaq Usman Kasai, shugaban kungiyar Hada Kan Al'ummomin Birnin Gwari-Neja, ya tabbatar da cewa 'yan bindigar suna karkashin jagorancin jagoran 'yan ta'adda, Yellow Jamboros.

Har yanzu gwamnatin jihar bata fitar da wata sanarwa game da lamarin ba kuma hukumar 'yan sanda ba ta amsa tambayoyi kan faruwar lamarin ba.

Manoma na biyan 'yan bindiga haraji

A wani labarin, mun ruwaito cewa ‘yan bindigan da su ka addabi kauyukan Giwa, jihar Kaduna sun tursasawa manoma biyan kudi idan suna sha’awar girbe amfanin gonakinsu.

Manoman da ke zaune a kauyuka irinsu Kidandan da Galadimawa suna cikin masu biyan kudi domin su iya yin aiki a gonakinsu yayin da matsalar tsaro ta kara tsamari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.