Lakurawa: Abubuwan Sani Dangane da Sabuwar Kungiyar 'Yan Ta'adda da Ta Bullo a Arewa
Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana Lakurawa a matsayin ƙungiyar ta'addanci da ke da alaƙa da mayaƙan jihadi a yankin Sahel.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Ayyukan Lakurawa a yanzu sun koma barazana ga tsaron mutane musamman na yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Duk da cewa da farko an san su a matsayin makiyaya masu yawo, a yanzu an gano ainihin abin da ƙungiyar ta ƙunsa.
Bayyanar kungiyar Lakurawa a Najeriya
A cikin shekarar 2018, mazauna yankin Tangaza da Gudu na Sokoto sun nuna damuwa game da bayyanar gungun makiyaya da ba a saba gani ba a dazuzzukan da ke kusa da su, cewar rahoton HumAngle.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da cewa suna ɗauke da manyan makamai, tun da farko ƴan sanda sun bayyana su a matsayin makiyayan da suka fito daga Jamhuriyar Nijar, ba wai masu tayar da hankali ba.
Sai dai, lamarin ya sauya a cikin ƴan kwanakin nan lokacin da hedkwatar tsaro ta ƙasa ta ayyana Lakurawa a matsayin "sabuwar ƙungiyar ta'addanci."
Su wanene ƴan Lakurawa?
Lakurawa sun fara ne a matsayin gungun makiyaya waɗanda a cewar mazauna yankin sun zo ne daga ƙasar Mali, suna jin Fulfulde da Larabci kuma suna da tarihin tayar da fitina.
Ƙungiyar ta yi gaggawar kafa sansanoni a kusa da kan iyakar Najeriya, musamman a Sokoto, domin yaɗa aƙidu masu tsattsauran ra'ayi ta hanyar fakewa da sunan kare al'umma.
Alhaji Aminu Dikko Tangaza wani mazaunin Tangaza ya bayyana cewa da farko ƴan Lakurawa sun riƙa ba su kariya daga ƴan bindiga, kafin daga bisani suka rikiɗe suka koma wani abu daban.
"Ƴan Lakurawa sun zo a matsayin makiyaya amma cikin hanzari suka fara nuna alamun ta'addanci."
"Da farko sun kare mu daga ƴan bindiga amma ba da jimawa ba suka ɓullo da wasu baƙin dokoki sannan suka fara neman kuɗi da shanu domin sayen makamai."
- Alhaji Aminu Dikko Tangaza
Lakurawa: Daga masu ba da kariya zuwa ƴan ta’adda
Domin yaƙar ƴan bindiga, wasu shugabannin yankin sun gayyaci ƴan Lakurawa domin su taimaka a harkar tsaro, wanda ya haɗa da horar da matasa.
Sai dai, ba da daɗewa ba dangantaka ta yi tsami yayin da ƴan Lakurawa suka fara sanya tsauraran dokoki na musulunci a kan al'ummomin da suke iƙirarin ba kariya.
Alhaji Magajin Balle, wani basarake a yankin ya bayyana cewa tun da farko sai da ya yi gargaɗi kan yin aiki tare da ƴan Lakurawa.
"Shawarata ita ce ka da mu bar matasanmu su shiga ciki, amma wasu shugabanni suka dage sai an yi hakan."
"Daga baya sun fara fuskantar matsaloli lokacin da ƴan ƙungiyar suka fara karɓar zakka da sanya sababbin dokoki ga mutanenmu."
- Magajin Balle
Yadda ƴan ƙungiyar Lakurawa ke gudanar da harkokinsu
Kamar yadda BBC Pidgin ta ruwaito, ƙungiyar Lakurawa na yaɗa saƙonninta ta hanyar yi wa mutane wa'azi, tare da gaya musu cewa ba su son yin alaƙa da ƴan sanda, sojoji, ƴan siyasa ko jami'an gwamnati.
Har ila yau, suna nuna adawa sosai ga ilimin boko. Wata majiya ta bayyana cewa ƴan ƙungiyar masu ɗauke da makamai na magana da mutane cikin yaruka daban-daban.
Rahotanni sun nuna cewa lokacin da suke wa’azi ko koyarwa, suna fassara saƙonsu zuwa Hausa, Fulfulde, Azbinanci, Turanci, da sauran harsuna.
Majiyar ta ce kimanin watanni takwas da suka gabata, bayan da jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar suka fatattake su, ƙungiyar ta koma yankin Sokoto.
Da farko mutane sun ji daɗin zuwan ƙungiyar domin sun kashe ƴan bindiga da suka addabi wasu yankuna Sokoto tare da ƙwace makamansu.
Majiyar ta ƙara da cewa ƴan ƙungiyar na hukunta matasan da suka yi shiga wacce ba ta dace ba ko askin banza.
Farmakar sojoji da yi wa mutane barazana
Ta'addancin Lakurawa ya fito fili ne a ranar, 10 ga watan Agusta lokacin da suka farmaki sansanin sojoji a Sokoto, inda suka hallaka sojoji uku.
Tun daga nan, sun mayar da hankali wajen kai hare-hare ga jami'an tsaro na gwamnati da sauran ƙungiyoyin da ke adawa da su yayin da suke ƙƴale fararen hula da suka amince da aƙidunsu.
Rundunar sojojin Najeriya ta yi martani ta hanyar bayyana shugabannin Lakurawa guda tara a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo.
Daga cikinsu akwai Abu Khadijah, Abdurrahman, da Musa Wa’a, wadanda ake zargin su ne ke jagorantar tashe-tashen hankula a Sokoto.
Tasirin Lakurawa a yankunan karkarar Sokoto
Lakurawa suna aiki ne ta hanyar sanya tsoro tare da kafa sansanonin "Darul Islam" inda suke koyar da nau'in ta su shari'ar Musuluncin.
Suna yin wa’azi da harshen Hausa da Fulfulde, tare da ɗaukar samari masu shekaru 18 zuwa 35 domin ba su horaswa.
Lakurawa na ɗaukar matasa
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan ƙungiyar Lakurawa sun fara ɗaukar matasa domin su shiga cikinsu a jihar Sokoto.
Rahotanni sun bayyana yadda yan ta'addan Lakurawa su ke amfani da tsatstsauran ra'ayi irin na Boko Haram wajen jan matasa domin su shiga cikinsu.
Haka kuma Lakurawan na tara matasa su na basu kudi masu tarin yawa domin su rungumi ra'ayin da su ka zo da shi, musamman a Sokoto.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng