Ana Zargin Ɗiyar Tsohon Gwamnan Arewa da Wulakanta Naira, EFCC Ta Gano Masu Laifin

Ana Zargin Ɗiyar Tsohon Gwamnan Arewa da Wulakanta Naira, EFCC Ta Gano Masu Laifin

  • Hukumar EFCC ta gudanar da bincike kan wani bidiyo da aka yada wanda ya nuna ana wulakanta Naira a wani biki a Kano
  • An zargi Fauziya, diyar Sanata Danjuma Goje da wulakanta Naira, amma EFCC ta gano cewa ba a wajen bikinta abin ya faru ba
  • Hukumar EFCC ta bayyana wadanda ake zargin sun aikata wannan laifi, kuma ta bukaci ango da danginsa su gurfana a ofishinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta yi martani kan wani bidiyo da ke yawo, inda ake zargin an ci zarafin Naira a wani biki a Kano a ranar 24 ga Oktoba.

An zargi Fauziya Danjuma Goje, diya ga Sanata Muhammad Danjuma Goje, da cin zarafin naira a yayin bikin, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce.

Kara karanta wannan

Damina ba ta kare ba: NiMet ta fadi jihohin da za a sheka ruwan sama na kwanaki 3

EFCC ta yi magana kan bidiyon wulakanta Naira a wani biki a jihar Kano
Diyar Sanata Goje: Hukumar EFCC ta gano bikin da aka wulakanta Naira a Kano. Hoto: Muhammadu Adamu Yayari
Asali: Facebook

A wani sako da ta wallafa a shafinta na X a ranar 11 ga Nuwamba, hukumar EFCC ta ce ta dauki matakin gaggawa na bincike bayan bullar wannan bidiyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar EFCC ta wanke diyar Sanata Goje

Sai dai kuma, bayan nazarin da ta yi wa bidiyon da ake yadawa, hukumar ta tabbatar da cewa an wulakanta Naira, amma ba a bikin diyar Goje ba.

EFCC ta ce an ci zarafin kudin kasar ne a wajen bikin Amina Babagana Zannah, diya ga Hajara Seidu Haruna, shugabar kamfanin gwala-gwalai na Hafsat Jewellery.

"Hajara Seidu Haruna ta tabbatar da bidiyon da ake yadawa kuma ta amince cewa an ci zarafin zarafin Naira a taron cin abincin bikin diyarta a ranar 24 ga Oktoba."

- A cewar sanarwar EFCC.

EFCC ta gayyaci angon Amina Zannah

EFCC ta ce mijin Amina, Ibrahim Mohammad, dan kasar Nijar ne, kuma wadanda ake zargin sun watsa takardun kudin sun fito ne daga dangin angon.

Kara karanta wannan

'Babu wanda ya isa': Ministan Tinubu ya lashi takobin rusa gidajen mutane a Abuja

Hukumar ta bayyana cewa ta bukaci mijin amaryar daga Nijar, Mohammad, da ya taho da wadanda suka watsa kudin zuwa hedkwatarta da ke Abuja.

Yayin da EFCC ke kokari wajen yaki da cin zarafin Naira, hukumar ta ce za ta tabbatar an hukunta wadanda aka samu da laifi, ko da kuwa suna da matsayi mai girma.

Wulakanta Naira: Sanata Goje ya magantu

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Gombe, Sanata Danjuma Goje ya musanta cewa an wulakanta Naira a bikin ‘yar sa, Fauziyya da angonta, Aliyu.

A sanarwar da hadimin Sanatan, Muhammad Adamu Yayari ya fitar, ya ce ana yada bidiyon watsa kudi a bikin Fauziyya ne domin a batawa iyalan Goje suna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.