Rundunar Yan Sanda Ta Yi Karin Bayani, Ta Fadi Wanda Ta Kama Lokacin Zanga Zanga
- Rundunar yan sandan Najeriya ta ƙaryata masu cewa an kama yara masu ƙananan shekaru a lokacin zanga-zanga
- Sufeton yan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun ne ya musanta zargin tare da bayanin ainihin wadanda aka kama lokacin
- Kayode Egbetokun ya kara da cewa dukkanin wadanda aka kama sun aikata laifin ta da tarzoma ko satar kayan jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Rundunar yan sandan Najeriya ta kara musanta cewa jami'anta sun kama yara masu kananun shekaru yayin zanga zangar adawa da manufofin gwamnati.
Matasan kasar nan maza da mata ne su yi fitar ɗango zuwa tituna na tsawon nuna bacin ransu kan yunwa, tsadar abinci da hauhawar farashin kayan amfanin yau da gobe.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a martanin da ya yi, Sufeton yan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun ya karyata cewa an kama ƙananan yara a lokacin zanga zangar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga zanga: Yan sanda sun yi bayanin kame
Jaridar The Nation ta wallafa cewa Sufeton yan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun ya ce jami'ansu sun kama masu laifi ne lokacin zanga-zanga.
Ya ce haka kuma an kama masu satar kayan jama'a da fasa shaguna tare da tayar da hankula a lokacin zanga-zanga.
"Ba mu kama masu zanga zanga ba:" Yan sanda
Rundunar yan sandan Najeriya ta musanta cewa ta kama masu gudanar da zanga-zanga zuwa ta lumana a fadin kasar nan.
Rundunar ta na wannan batu ne bayan sakin wasu yara masu ƙananan shekaru da aka gurfanar a gaban babbar kotun tarayya bisa zargin cin amanar kasa.
An saki yara da aka tsare da zanga zanga
A baya mun wallafa cewa gwamnatin tarayya ta janye tuhumar cin amanar kasa da yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu da ake yi wa wasu yara da matasan da su ka yi zanga-zanga.
Bayan sakin wasu yara da bidiyon halin da su ke ciki ya fusata yan Najeriya, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya mika yan asalin Kano daga cikin yaran ga gwamna Abba Kabir Yusuf.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng