Bayan Karbar 'Yan NNPP, Sanata Barau Ya Gwangwaje Shugabannin APC
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya gwangwaje shugabannin jam'iyyar APC a jihar Kano da sha tara ta arziƙi
- Sanata Barau Jibrin ya raba motoci da babura ga shugabannin jam'iyyar APC a matakin jiha, shiyya, ƙaramar hukuma da mazaɓu a faɗin Kano
- Rabon ababen hawa da Sanata Barau ya yi na zuwa ne yayin da yake ci gaba da karɓar masu sauya sheƙa daga jam'iyyar NNPP zuwa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - A ci gaba da ƙoƙarin bunƙasa harkokin APC, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya gwangwanje shugabannin jam'iyyar da ababen hawa a Kano.
Sanata Barau Jibrin ya ba shugabannin jam'iyyar APC a jihar Kano tallafin motoci 61 da babura 1137.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Shitu Madaki Kunchi, mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a ga Sanata Barau ya fitar, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barau Jibrin ya ba shugabannin APC motoci
Ya ce an raba motoci 61 ga shugabannin jam’iyyar da suka haɗa da na dukkanin ƙananan hukumomi 44, shiyyar Kano ta Arewa, Tsakiya da Kudu, da kuma ofishin jam’iyyar APC na jihar, rahoton jaridar Blueprint ya tabbatar.
"Bugu da kari, an shirya samar da babura 1137 ga shugabannin mazaɓu domin sauƙaƙa zirga-zirgarsu da kuma inganta ayyukan jam'iyyar.
"Da hakan Sanata Barau ya sake jaddada ƙudirinsa na ci gaba da tallafawa shugabannin APC da ƴaƴan jam’iyyar, inda ya yi alƙawarin ci gaba da bayar da goyon baya don tabbatar da haɗin kan jam’iyyar da samun nasara a faɗin jihar."
- Shitu Madaki Kunchi
Sanata Barau ya shirya karɓe Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce jam’iyyar APC za ta karbe mulkin jihar Kano a babban zabe mai zuwa.
Sanata Barau ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana kan nadin Yusuf Abdullahi Ata daga Kano a matsayin minista a zauren majalisar dattawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng