Yaƙi da Lakurawa: Tawaga daga Arewa ta Gana da Hafsun Tsaro

Yaƙi da Lakurawa: Tawaga daga Arewa ta Gana da Hafsun Tsaro

  • Tawaga mai karfi daga Arewa maso Yamma ta gana da babban hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa kan yaki da Lakurawa
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamna Nasir Idris na Kebbi ne ya hada tawagar kasancewar Lakurawa sun fara ta'addanci a jiharsa
  • Hafsun tsaro, Janar Christopher Musa ya tabbatarwa tawagar da cewa sojojin Najeriya ba za su yi kasa a gwiwa ba kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Gwamna Nasir Idris ya haɗa tawaga ta musamman domin ganawa da hafsun tsaro, Janar Christopher Musa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa tawagar ta gana da hafsun tsaron ne game da sabuwar kungiyar yan ta'addar Lakurawa da ta bullo a Arewa.

Kebbi
Tawagar Kebbi ta gana da hafsun tsaro. Hoto: @KBStGovt
Asali: Twitter

Gwamnatin jihar Kebbi ta wallafa a X cewa Janar Christopher Musa ya tabbatarwa tawagar cewa ba za su yi wasa ba wajen yaki da yan ta'addar.

Kara karanta wannan

'Cututtuka na shigowa Najeriya saboda yunwa,' NLC ta tono bayanai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tawagar Arewa ta gana da hafsun tsaro

Gwamnan Nasir Idris ya tura tawaga wajen Janar Christopher Musa domin neman hanyar yakar Lakurawa.

Gwamnan ya tura tawagar da bukatar neman daukar matakin gaggawa a kan yan ta'addar da suka ɓulla a Sokoto da Kebbi.

Jagororin tawagar sun yi godiya ga sojojin Najeriya bisa yadda suke ba da hadin kai a kan yaki da yan bindiga a Arewa ta yamma.

Tawagar da ta gana da hafsun tsaro

The Nation ta wallafa cewa a cikin tawagar akwai ministan kasafin kudi, Atiku Bagudu da Sanata Bala Ibn Na'Allah.

Haka zalika akwai sakataren gudanarwan APC na kasa, Sulaiman Argungu da tsohon Kwamishinan shari'a na Kebbi, Nasiru Junju.

Hafsun tsaro ya ce za a yaki Lakurawa

Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya tabbatarwa tawagar cewa a shirye suke wajen yaki da yan ta'addar.

A yayin wata ziyara da ya kai Sokoto, mukaddashin shugaban sojojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Olufemi Oluyede ya yi alkawarin gamawa da Lakurawa.

Kara karanta wannan

Lakurawa sun gano hanyar daukar matasa cikin sauki, ta'addanci zai ƙaru

Sojoji sun hallaka 'yan Lakurawa

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare kan maɓoyar ƴan ta'adda a jihohin Kebbi da Zamfara.

Jami'an tsaron sun hallaka ƴan ta'adda masu tarin yawa ciki har da na sabuwar ƙungiyar Lakurawa da ta bayyana a cikin ƴan kwanakin nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng