Sanata Ya Ga Halin da Talakawa ke Ciki, Ya Nemi Mafita daga Shugaba Tinubu
- Sanata Babangida Hussaini ya bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakin kawo karshen tsadar abinci
- Ya bayyana cewa ya ga halin da talakawa ke ciki duk da cewa lokaci ne na samun arharsa tun da an fara girbe abinci a gonaki
- Sanata Babangida Hussaini da ke wakiltar mutanen shiyyar Arewa ta Yamma a Jigawa, ya ce akwai babbar matsalar abinci a kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Jigawa – Sanata mai wakiltar Jigawa shiyyar Arewa ta Yamma, Babangida Hussaini ya bayyana irin matsalar da jama'ar kasa ke ciki.
Ya shaidawa gwamnatin Bola Tinubu cewa jama’a su na cikin matsananciyar yunwa da tsadar abinci duk da cewa kaka ta kama.
Jaridar Punch ta wallafa cewa dan majalisar, ya bayyana cewa bai dace a rika samun tashin farashin abinci a lokacin kaka ba, duba da cewa akwai wadatar abinci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsadar abinci: Sanata ya nemi daukin Tinubu
Sanata Babangida Husaini ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi su tashi tsaye kan tsadar abinci.
Jaridar Aminiya ta ruwaito Sanatan ya bayyana yadda ya gano ana samun hauhawar farashin kayan abinci a sassan kasar nan bayan an fara girbe abinci daga gonaki.
Sanata ya koka kan tsadar rayuwa
Dan majalisar dattawa mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso Yamma ya ce yan kasar nan na fama da matsin rayuwa gami da tsadar abinci.
“Wannan, hadi da matsin tattalin arziki da jama’a ke ciki abin tsoro ne, musamman a farkon lokacin girbi da ya kamata a samu abinci da araba,” cewar Sanata Babangida Husaini.
Ya dora alhakin matsalar da ake samu a kan rashin tsaro da garkuwa da mutane a garuruwan da ke noma a kasar nan.
Sanata ya bijrewa manufofin Tinubu
A baya kun ji cewa Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume ya zargi gwamnatin tarayya da bijiro da kudurorin da ke hana talakawa walwala a fadin kasa.
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa zai yi duk abin da ya dace wajen bijrewa sabon kuduri na karin haraji da Bola Tinubu ya ke kokarin kakabawa kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng