Damina ba Ta Kare ba: NiMet Ta Fadi Jihohin da za a Sheka Ruwan Sama na Kwanaki 3

Damina ba Ta Kare ba: NiMet Ta Fadi Jihohin da za a Sheka Ruwan Sama na Kwanaki 3

  • Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen saukar hazo da ruwan sama a jihohin Kudu da Arewacin kasar nan
  • Daga Litinin, 11 zuwa Laraba 13 ga watan Nuwamba, NiMet ta ce hazo zai sauka da zai hana ganin nesa daga nisan kilomitoci
  • Za a fuskanci tsawa da ruwan sama a jihohi kamar Legas, Akwa Ibom da Cross River, kamar yadda rahoton hukumar NiMet ya nuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen gurɓataccen hazo da ruwan sama a fadin Najeriya daga Litinin zuwa Laraba.

Hukumar ta yi hasashen samun hazo marar kauri a Arewacin kasar, wanda zai iya hana masu ababen hawa ganin gabansu daga nesa.

NiMet ta yi hasashen yanayin kwanaki 3 a jihohin Kudu da Arewa
Hukumar NiMet ta bayyana jihohin da ruwan sama da hazo zai sauka a kwanaki 3. Hoto: NurPhoto / Contributor
Asali: Getty Images

A yankin Arewa ta Tsakiya, ana hasashen samun hango marar kauri, inda masu ababen hawa za su iya ganin gabansu da tazarar kilomita 2 zuwa 5, a cewar rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya karfafi yan Najeriya, ya yi kyakkyawan albishir

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hasashen NiMet na ranar Litinin

Sai dai kuma, rahoton NiMet ya nuna cewa yankin Kudu zai fuskanci rana tare da yanayi mai hazo.

NiMet ta yi hasashen iska da tsawa gami da ruwan sama a jihohin Legas, Akwa Ibom da Cross River a safiyar yau.

Haka kuma, hukumar ta ce ruwan sama da tsawa za su kara ta'azzara a yammacin ranar Litinin a jihohin Kudu.

Hasashen hazo da hadari a ranar Talata

A ranar Talata, yankin Arewa zai fuskanci buji wanda zai hana ganin nesa daga nisan kilomita 2 zuwa 5. Arewa ta Yamma da ta tsakiya za su fuskanci hakan.

Yankin Kudu zai fuskanci rana mai hazo tare da ruwa musamman a jihohin bakin teku. Hakanan, ana sa ran samun gurɓataccen hazo mai takaitaccen tasiri.

Hasashen NiMet na ranar Laraba

Hasashen ranar Laraba ya nuna bayyanar hazo da zai hana hangen nesa na kilomita 2 zuwa 5 a yankin Arewa. A yankin Kudu, ana sa ran samun hazo mai haske.

Kara karanta wannan

Tsadar fetur: Mazauna Kano sun hakura da hawa mota, sun nemawa kansu mafita

Daily Post ta rahoto cewa ana sa ran samun tsawa da ruwan sama mai tsanani a sassan Legas, Rivers, Bayelsa da Akwa Ibom.

Hukumar NiMet ya yi kira ga jama'ar wadannan yankuna da su dauki matakan kariya ta hanyar amfani da makaran numfashi saboda hazo.

Za a yi ruwan sama a jihohin Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar NiMetz ta yi hasashen cewa za a zabga ruwan sama hade da tsawa a wasu jihohin Kudu da Arewacin kasar nan.

A cewar NiMet, ana sa ran za a yi ruwa da tsawa a wasu sassan jihohin Bauchi, Adamawa, Kaduna, Katsina, Taraba, Yobe, Zamfara, Borno da Kebbi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.