Hukumar NIMET ta ce za a ga iskar buji mai duhu a wasu Yankuna

Hukumar NIMET ta ce za a ga iskar buji mai duhu a wasu Yankuna

Hukumar NiMet mai binciken yanayi a Najeriya ta gano irin yanayin da za a tashi da shi a Yau Ranar Lahadi, 5 ga Watan Junairu, 2019.

A na ta tsinkayen da ta yi, NiMet ta na sa ran cewa za a cigaba da ganin iskar buji mai karfi a jihohin Arewacin Najeriya a yau dinnan.

NiMet ta hango iska mai kauri a fadin jihohin da ke Arewa zuwa tsakiyar kasar. Hukumar ta yi wannan bayani ne a jiya Ranar Asabar.

A jawabin da hukumar ta fitar a babban birnin tarayya Abuja, ta ce matsakaicin hazo zai rika yawo ta yadda za a iya hangen kilomita 1-3.

“A jihohin Arewa, ana sa ran ganin iska mai karfi a lokacin da aka yi hasashe. A cikin dare sanyi zai kai maki 6 zuwa 12 na Digirin Celsius.”

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta yi karin farashin wutan lantarki

Hukumar ta cigaba da cewa: “Da wayewar Gari, za a fuskanci yanayin sanyi daga maki 20 zuwa 28 na Digirin Celsius a wadannan wurare.”

A jihohin Kudu kuma yanayin iskar da za a samu matsakaiciya ce wanda zai kai mutum ya hangi tafiyar kilomita 1-3 a gabansa Inji NiMet.

“Ana sa ran cewa yanayin sanyin Gari a lokacin rana zai kai maki 29 zuwa 36 na Digirin Celcius, da kuma maki 11 zuwa 22 a cikin dare.”

Kawo yanzu dai mun samu labari cewa mutanen Garuruwa irinsu Funtuwa, Jos, Zaria, Kano, da sauransu, su na kukan sanyi ya yi kamari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel