Tsadar Fetur: Mazauna Kano Sun Hakura da Hawa Mota, Sun Nemawa Kansu Mafita

Tsadar Fetur: Mazauna Kano Sun Hakura da Hawa Mota, Sun Nemawa Kansu Mafita

  • A jihar Kano, hauhawar farashin man fetur ya tilastawa mazauna garin amfani da kekuna, baburan lantarki ko tafiya a kasa
  • Rahoto ya nuna cewa an samu karancin motoci a kan titunan jihar Kano yayin da jama'a ke neman sauki kan tsadar rayuwa
  • Dalibai, ma'aikatan gwamnati da 'yan kasuwa sun koma amfani da wasu hanyoyin sufurin domin tattalin 'yan kudinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Hauhawar farashin litar fetur zuwa N1,150 ya sa mazauna Kano daina amfani da motoci tare da nemawa kansu wasu hanyoyin sufuri na daban.

Mazauna Kano yanzu suna apmfani da hanyoyin sufuri kamar tafiyar kasa, keke da baburan lantarki yayin da aka lura da karancin motoci a kan tituna.

Mazauna Kano sun nemawa kansu mafita a harkar sufuri bayan tsadar fetur
Tsadar fetur ta sa mazauna Kano daina amfani da motoci, sun nemi wata mafitar. Hoto: Jorge Fernández / Contributor
Asali: Getty Images

Mazauna Kano sun hakura da motoci

Sani Isa, a wata hira da jaridar Daily Trust, ya ce hauhawar farashin man fetur ya shafi kudin sufurinsa na yau da kullum, inda yanzu yake kashe N1,200 a kowace rana.

Kara karanta wannan

‘Yan adawa sun fara yabawa a Kano, Abba ya yi bayanin yadda yake inganta lantarki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Sani, wanda mazaunin Kano ne, ya ce ya hakura da hawa mota, ya koma amfani da keke, wanda ya ke ganin ya fi sauki da araha.

Dalibai kamar Aminu Ishaq sun koma amfani da kekuna a matsayin hanyar sufuri mai araha.

Aminu, wanda ke karatu a Kwalejin Ilimi ta Kano, ya ce ya samu sauki wajen zuwa makaranta a kan lokaci, inda a gefe daya yake adana 'yan kudin shi.

Keke mai lantarki ya fara samun karbuwa

Wani ma’aikacin gwamnati, Muhammad Sadiq ya bayyana cewa ya koma takawa a kafa daga gida zuwa sakatariyar gwamnatin tarayya sannan yana hawa keke Napep daga can.

Ali Abdullahi, wani mazaunin garin, ya gano cewa baburan lantarki sun fi dacewa da tsarin tattalin da ake ciki yanzu. Ya ce ya sayar da wata motarsa ya sayi babur din.

Wani dan kasuwa Tasi’u Murtala shi ma ya sayi babur mai lantarki. Ya bayyana cewa babur din, idan aka caja shi, zai iya yin tafiyar kilomita 60 kafin a sake cajinsa.

Kara karanta wannan

Jerin kasashen Afrika 5 da suka fi bata lokaci a kafofin sadarwa ta zamani

Ya bayyana cewa a baya yana kashe N5,000 a kowace rana a sayen fetur, amma yanzu yana kashe kudi kadan bayan sayen babur mai lantarki a kan N750,000.

Ƴan Kano sun nemawa kansu mafita

Karuwar amfani da baburan lantarki yana kara samun karbuwa saboda araha da fa’idar muhalli da hakan bayarwa.

Yayin da farashin man fetur ke ci gaba da tashi, ana sa ran mazauna garin Kano za su ci gaba da nemawa kansu hanyoyin sufuri na daban.

Tun a yanzu an fara ganin sauyi, yayin da motoci suka rage yawo a kan titunan jihar, inda mutane ke takawa a kasa, ko hawa keke, ko amfani da baburan lantarki.

Mazauna Kaduna sun koma hawa jirgi

A wani labarin, mun ruwaito cewa mazauna jihar Kaduna, sun hakura da hawa motocin gida, inda suka koma bin jirgin kasa zuwa birnin tarayya Abuja.

An rahoto cewa tsadar fetur ta tilastawa fasinjojin Kaduna komawa hawa jirgin duk da irin tsoron da ake ji na hawan jirgin bayan hare-haren da ya fuskanta a baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.